A yanzu haka dai akwai wani daftarin dokar tantancewa da bin kadin wa’azi da ke gaban Majalisar Jihar Kaduna, wacce a cikinta ake neman ta kwafe makamanciyarta da aka kafa a 1984. A sabuwar dokar nan, tana nufin ta samar da hanyoyin tantancewa da bin kadin wa’azin addinai, yadda za a riva hukunta duk wanda ya karya va’idoji da tanade-tanadenta. Sai dai kuma ita wannan sabuwar doka, tana fuskantar tarnavi da suka daga malaman addinan Musulunci da Kirista.
Ita dai wannnan sabuwar doka idan ta tabbata, ya zama wajibi ga duk wanda ke son yin wa’azin addini sai ya nemi izinin hukumar Jihar Kaduna, ta tantance shi sannan ta ba shi lasisi. Kuma shi wannan lasisi, za a riva sabunta shi a kowace shekara. Haka kuma dokar ta haramta saka faya-fayan wa’azi a bainar jama’a, sannan kuma za a riva amfani da lasifika ne kawai a cikin masallatai da coci-coci kadai, su ma din kada a wuce varfe takwas na dare. Don haka duk wani wa’azi a tituna laifi ne, sai dai a masallatai da coci-coci. Duk wanda ya karya dokar kuma, za a hukunta shi, ta cin tarar Naira dubu 200.
Wani abin da dokar ta vunsa kuma shi ne, duk mai wa’azin da hukuma ta ankara da cewa yana kawo sabani da rashin jituwa ko zai iya tada hargitsi, za ta iya soke lasisinsa kuma za a iya hukunta shi da daurin shekara biyu a gidan yari ko zabin tarar Naira dubu 200 ko kuma a hada masa duka.
Wasu malaman addini sun maida martani dangane da wannan doka, daya daga cikinsu shi ne Rabaran Emma Egoh, Mataimakin Shugaban Cocin Pentecostal (PFN) na Jihar Kaduna. A vorafinsa, ya zargi Gwamna Nasiru el-Rufa’i da cewa ya virviro wannan doka ne da nufin davile aikin masu wa’azi a jihar da kuma nufin takura wa malaman addini. Ya ce wannan doka ta saba wa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 dangane da havvin ’yan vasa na gudanar da addininsu ba tare da takurawa ba. Mai ba tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero shawara, Sheikh Haliru Maraya, ya bayyana dokar da cewa bata lokaci ne da bata dukiya. Ya ce: “Musulunci ya ba kowane Musulmi ’yancin gudanar da addininsa, kamar dai yadda sashi na 38 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya ba kowane dan Najeriya irin wannan dama.”
Shi kuwa Babban-Daraktan hukumar kula da al’amuran addinai a Jihar Kaduna, Injiniya Namadi Musa ya ce an virviro dokar ce bisa la’akari da yadda al’umma ke vorafi dangane da yadda wasu masu wa’azi ke wulavanta wasu shugabannin addinai, wani lokacin ma har da addinan da ba nasu ba, kamar kuma yadda al’umma ke vorafi dangane da yadda ake hana su sukuni da varar lasifikoki da makamantansu da tsakar dare. Ya ce ita wannan doka ba za ta hana kowa gudanar da addininsa ba.
Mu dai a nan, muna ganin cewa abu ne mai muhimmanci a riva tantance masu wa’azi domin barin wadanda suka cancanta kawai, musamman idan aka yi la’akari da yanayin vasar nan; inda za ka ga hatta wadanda ba su da isasshen ilimin addini amma suna yin wa’azi. Idan mun lura, Jihar Kaduna ma ta sha bamban da sauran jihohi, domin tana dauke da mabiyan mabambamtan addinai da avidoji, don haka ya zama dole a yi taka-tsan-tsan wajen tafiyar da al’amuran addinai a jihar. Sai dai muna ganin ba wani abu ya kawo rashin fahimta a dokar ba, illa rashin halartar masu ruwa da tsaki a al’amuran addinai, yayin gudanar da taron tsara dokar. Yadda aka samu vorafi da rashin amincewar wasu daga vungiyoyin addinan Musulunci da Kirista, ba zai rasa nasaba da yadda Gwamnatin Kaduna ta bullo da al’amarin ba, inda ba ta wayar da kan al’umma dangane da haka ba, kafin ta fito da batun. Domin kuwa da kamata ya yi a ce an gayyace su, an tattauna kuma an nemi shawarwari daga gare su tun da farko.
A yayin da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya ba kowane dan vasa ’yancin gudanar da addininsa, ita wannan doka ta Jihar Kaduna tana nufin tantancewa da bin kadi ne. Idan za mu dauki misali, annobar Boko Haram ta faru ne sanadiyyar rashin kula da tantancewa a hukumance ta fuskar al’amuran addini, wanda haka ya ba shugaban vungiyar Muhammad Yusuf damar barbaza karkatattar avidarsa ga al’umma. Don haka mu a nan, muna goyon bayan Gwamnatin Jihar Kaduna, dangane da fito da dokar tantancewa da bin kadin al’amuran wa’azin addinai. Sai dai ya kamata kafin a zartar da dokar, a tuntubi shawarwarin masu ruwa da tsaki ga addinai da sauran al’umma, domin samun gamsassun bayanai da za su taimaki dokar.
Dokar tantancewa da bin kadin wa’azin addinai a Jihar Kaduna
A yanzu haka dai akwai wani daftarin dokar tantancewa da bin kadin wa’azi da ke gaban Majalisar Jihar Kaduna, wacce a cikinta ake neman ta…