✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar rufe fuska: ‘Buhari bai saba doka ba’

Shugaba Muhammadu Buhari ba ya saba doka don ba ya sanya kyallen rufe fuska, a cewar mai taimaka masa kan kafofin sada zumunta na zamani, Lauretta…

Shugaba Muhammadu Buhari ba ya saba doka don ba ya sanya kyallen rufe fuska, a cewar mai taimaka masa kan kafofin sada zumunta na zamani, Lauretta Onochie.

Onochie ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Asabar.

Ta ce masana harkar lafiya sun bayyana cewa ba lallai ba ne sai mutum ya yi amfani da kyallen matukar yana muhallin da aka tabbatar babu kwayar cutar ko barazanarta.

“Shugaba Muhammadu Buhari bai karya doka ba! Ka’idar Kwararrun Masana Kiwon Lafiya ita ce idan kana wuri lafiyayye, ba ka bukatar ka saka kyallen rufe fuska.

“Wadanda suka kawo maka ziyara ne ya WAJABA su saka don tabbatar da cewa ba su bar maka digon [kwayar cutar] ba.

“Galibi muna saka kyallen ne don mu kare mutanen da ke kewaye da mu”, inji ta.

Wasu masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum dai sun soki Shugaba Buhari saboda rashin amfani da kyallen a tarukan da ya gudanar har sau biyu a ‘yan kwanakin nan, duk kuwa da umurnin da ya bayar na tilasta yin hakan a duk fadin kasa.

Wasu dai na kallon abin da shugaban kasar ya yi a matsayin na mai dokar barcin da yake kokarin bigewa da gyangyadi.