Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya ce matakin hana yawon kiwo da wasu gwamnoni suka dauka ba ya aiki.
Gwamna Sule ya fadi haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels.
- Yunwa Ta Sa ’Yan Bindiga Fara Shirin Satar Amfanin Gona – Masari
- Masu Neman Sarautar Kwantagora Sun Nemi A Sake Sabon Zabe
“Ba ma son wannan manufar ta hana yawon kiwo, ba ta aiki,” in ji shi
“Ba za mu bi yarima mu sha kida ba game da dokar hana yawon kiwo. Idan ka sanya hannu a kan dokar hana kiwo kuma ba ta aiki, mene ne amfaninta?”
Sai dai duk da haka, Sule ya ce yawon kiwo da makiyaya ke yi ba abu ba ne mai dorewa.
“Abu guda da gwamnonin Arewa muka yanke shawara a kai shi ne yawon kiwo tsohon yayi ne, kuma ba zai dore ba”, in ji shi.
– A madadin hana kiwo…
Ya kara da cewa a madadin dokar hana yawon kiwo, Jihar Nasarawa ta yanke shawarar amincewa da Tsarin Habaka Kiwon Dabbobi na Kasa.
Ya yi bayanin cewa gwamnatinsa ta yi shirin tsugunar da makiyaya ta hanyar kakkafa gandun kiwon dabbobi a wurare bakwai a cikin jihar tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya da Gwamnatin kasar Holland.
“Hanya mafi inganci ta yin hakan ita ce idan kuna da zai don mutane; abu ne mai sauki mu je majalisar dokoki mu nemi a yi dokar hana kiwo.
“Amma me zai faru da Fulanin da ke kai-kawo? Idan Fulanin sun san abin da ya sa dokar ba ta aiki, ba su wani abu mai aiki shi ne abu mafi a’ala, ”inji shi.
Gwamnonin jihohin Enugu, da Ribas, da Akwa Ibom, da Ondo da Legas sun sanya hannu a kan dokar hana kiwo.
Wannan ya biyo bayan kudurin da aka cimma a taron Kungiyar Gwamnonin Kudu.
Gwamnonin Kudancin dai sun tsayar da 1 ga watan Satumba, 2021, a matsayin ranar da za a sanya hannu a kan dokar.