Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta ce za ta fara aiwatar da dokar hana sayar da man fetur a cikin jarkoki da sauran mazubai a fadin Jihar.
Kakakin Rundunar a Jihar, ASP Lawan Shiisu ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a Dutse, babban birnin Jihar ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, “Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Jigawa tana sanar da jama’a cewa an fito da sabbin matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
“Saboda haka, la’akari da sabuwar dokar Gwamnatin Jihar a kan hana sayar da man fetur, ana umartar dukkan masu gidajen mai da su daina sayar da mai a cikin jarka ko mazubin da ya kai lita 60 ga kowanne mutum ko kuma kungiya,” inji kakakin.
Rundunar ta ce duk gidan man da ya yi kunnen uwar shegu da dokar zai fuskanci fushin hukuma.
Ta kuma ce za ta hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro wajen lekawa kowanne lungu da sakon Jihar domin tabbatar da an bi dokar sau da kafa.
A ranar takwas ga watan Satumban 2021 ne dai gwamnatin Jihar ta haramta yin amfani da babura daga tsakanin karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe don dakile ayyukan ’yan ta’addan.
A ’yan kwanakin nan dai, Jihar ta Jigawa ita ma ta fuskanci rahotannin satar mutane, ciki har da na wani mai shekara 60 a Karamar Hukumar Taura.
Kazalika, an sace wani mai shakara 60 a gidansa da ke Zango a Karamar Hukumar Miga. (NAN)