Bisa al’ada, Dayyabu Sa’eed ba ya wuce karfe 11.00 na safe bai fita kasuwa ba.
A matsayinsa na Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Bulawus a Jihar Kano, ba ga harkokin kasuwancinsa kawai yake mayar da hankali ba, har ma ga na sauran ’ya’yan kungiya.
Don haka ne wayewar garin Juma’a yake jin kansa a cikin wani yanayi da bai saba shiga ba—a takure.
“Wallahi lamarin babu dadi”, inji shi, domin, “a yanzu haka akwai kayan ’yan kungiyarmu da ke hanya sun taso daga jihar Anambra”.
Sai dai kuma ba yadda aka iya—“Akwai abubuwa da dama da suke gabanmu a kasuwa wadanda dole ta sanya muka jingine su”—illa a san yadda za a taimaki wadanda idan ba su fit aba za su shiga halin ha’ula’i.
“Jiya sai da muka kai dare a kasuwa inda muka sayi kayan abinci muka raba wa masu karamin karfi da kuma leburori a cikinmu domin rage musu radadin zaman gidan da za a yi na tsawon mako guda”, inji Alhaji Dayyabu.
Shi ma Malam Umar Amin wani magidanci ne da ya bayyana zaman gidan a matsayin wani babban tashin hankali kasancewar bai saba zaman kulle ba.
“Zaman gida ba na namji ba ne, yau din nan kawai har na fara gajiya da zaman gidan ga surutun yara sun hana ni sakat! Kai abin dai babu dadi!”
Tuni dai jami’an tsaro, musamman ’yan sanda, suka mamaye manyan titunan birnin na Kano.
Sai dai Aminiya ta gano cewa duk da haka akwai wasu ’yan tsiraru da suka yi kunnen uwar shegu da dokar, suke zirga-zirga a wuraren da ba ’yan sanda, musamman Zaria Road.
Masu kantunan kayan masarufi a cikin unguwanni ma na ci gaba da hadahadarsu kamar yadda suka saba; a cewarsu bukata ce ta haifar da hakan.
Amma fa dukkan kasuwannin jihar a rufe suke, kamar yadda dokar ta tanada.
Gwamnatin jihar ta Kano dai ta ayyana dokar ne da nufin hana cutar coronavirus yaduwa, bayan da aka ba da rahoton mutuwar daya daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar.
Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa zuwa karfe 11.20 na daren Alhamis, mutum 21 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Kano.