Gwamnatin Jihar Taraba ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a garin Jalingo da Wukari bayan ’yan daba sun wawure kaya a ma’ajiyar kayan gwamnati.
’Yan daba sun wawure gidan saurkar baki da Sakatariyar Karamar Hukumar Wukari da Ma’aikatar Gona da dakin ajiyar kayan gwamnati a cikin dare inda suka yi awon gaba da dukiya ta miliyoyin Naira.
- An ba wadanda suka saci kayan tallafin Osun sa’a 72 su dawo da su
- Zanga-zangar EndSARS shiri ne na cin mutuncin Buhari —Rashida Mai Sa’a
Sun kuma mamaye gine-ginen da aka ajiye kayan tallafin COVID-19, takin zamani da sauran dukiyoyin gwamnati a Jalingo da Wukari suka kuma wawushe kayayyakin.
Matasan sun kuma farfasa shaguna da ma’ajiya mallakin daidaikun mutane a Jalingo lamarin da ya tilasta wa gwamnatin jihar tsawaita dokar hana fitar zuwa sa’a 24.
Aminiya ta lura an jibge karin ’yan sanda a Jalingo yayin da aka kafa shingayen bincike a wani bangare na garin.
Sai dai duk da dokar, gidajen mai da kamfanoni da baburan haya sun ci gaba da gudanar da ayyukansu.