Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana shirin kafa dokar auna kwakwalwar duk wani malami da yake da niyyar yin wa’azi a jihar don takaita irin tufka da warwarar da malaman suke yi.
Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar, Dokta Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kano.
- An kashe mutum biyu, an sace malamin tsangaya da wasu da dama a Zariya
- Tana kashe wa tantabaru 2 Naira miliyan 2 kan kayan kwalliya duk wata
Kwamishinan ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa na mika kudirin dokar yin wa’azi a jihar ga Majalisar Dokokin Jihar.
“Daga wannan ma’aikata za mu yi kudiri mu kai majalisa, mu kai Majalisar Zartarwa ta Jihar don ya zama doka. Duk malamain addinin da zai yi wa’azi sai ya kawo satifiket da yake nuna cewa kwakwalwarsa lafiya lau take kuma ba ya shayeshaye,” inji Kwamishinan.
Sai dai wannan magana ta Kwamishinan ta yamutsa hazo a jihar musamamn a tsakanin malamai wadanda suke da ra’ayin cewa ’yan siyasa ya kamata a auna wa kwakwalwa ba su ba.
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce batun auna kwakwalwar malamai bai ma taso ba. “Kamata ya yi a yi wa wadanda suke rike da shugabanci ko mukami kamar yadda tsohuwar Shugabar Hukumar EFCC, Hajiya Farida Waziri ta fada a baya da kuma abin da Sarkin Kano (murabus) Malam Muhamamdu Sanusi II ya fadi. ’Yan siyasa manya da kanana da ma’aikata manya da kanana su ne suka fi cancanta a fara auna kwakwalwarsu domin ana ganin irin abubuwan da suke aikatawa wadanda sun fi karfin a ce na hankali ne ko na tunani,” inji shi.
Shi ma Limamain Masallachin Ihyaussunnah da ke Gwammaja Sheikh Abubakar Abdussalam (Baban Gwale) ya ce yin dokar kuskure ne wanda kuma ya saba wa addini.
“Duk da cewa ba mu ga dokar mun karanta abin da ta kunsa ba. Amma in har abin da kafofin watsa labarai suke bayyanawa game da dokar haka yake za mu iya cewa wannan doka kuskure ne kuma ta saba wa addini. Babu masu hankali da suka kai malamai,” inji shi.