Wani kazamin fada tsakanin gungun ’yan bindiga na Dogo Gide da na Damina, kasurgumin dan bindigar nan da ke da sansani a dajin Kuyambana na Zamfara, ya yi sanadiyyar mutuwar Daminan.
Dan bindigar dai ana zarginsa da kasancewar kanwa uwar gamin da ya kitsa munanan hare-hare, garkuwa da mutane da satar shanu da ma tilasta wa mutane biyan haraji a yankuna da dama na masarautar Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar.
- Sojojin Najeriya sun kera manyan jiragen yakin ruwa guda 4
- Za mu fara yi wa masu yi wa kasa hidima rigakafin COVID-19 – NYSC
Ko a watan Yulin da ya gabata, Damina ya jagoranci kai hari garuruwan Tungar Bausheda kuma Randa, inda aka kashe mutane da dama sannan aka sace wasu kimanin 100, yawancinsu mata da kananan yara.
A nasa banagren kuwa, Dogo Gide, wanda ake zargi da hallaka Daminan shi ma wani kasurgumin dan bindiga ne da ya gagari kundila a yankin, wanda a shekarar 2017 ya kashe fitaccen dan bindigar nan, wato Buharin Daji a kusa da garin Dansadau.
Rahotanni dai sun ce Damina ya rasu ne sakamakon munanan raunukan da ya ji sakamakon ba-ta-kashin da aka yi da yaransa da na Dogo Giden a kusa da Chillin da Fammaje, wasu kauyuka biyu da suka kasance karkashin ikonsa.
Wasu majiyoyi a yankin sun shaida wa wakilinmu cewa Dogo Gide wanda aka yi ittifakin yana da alaka da kungiyar ISWAP ba ya jin dadin yadda Damina yake kai hare-hare tare da tashin kauyukan yankin.
Hakan, a cewar wasu mazauna yankin da suka saba da rikicin, ya sa Dogo Giden ya sha gargadinsa da ya daina kai hari yana kashe manoman da ba su ji ba, ba su gani ba, amma ya ki.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, wakilinmu bai samu jin ta bakin Gwamnatin Jihar kan batun ba, saboda Kwamishinan Tsaron Jihar, DIG Ibrahim Mamman Tsafe bai amsa kiran wayarsa ba.
Kazalika, wayar kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu ita ma ba ta tafiya.
To sai dai Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau, wanda dan asalin yankin ne ya tabbatar da rahoton kisan kamar yadda aka shaida wa wakilin namu.
“Gaskiya ne, Dogo Gide ya kashe Damina. Muna da bayani a kan haka, kuma tabbas ya faru,” inji shi.