✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogara ya tallafa wa kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i a Bauchi

Shugaban Majalisar Wakilai Honorabul Yakubu Dogara, ya ziyarci kasuwanni da dama a garuruwa da kauyukan da ke Jihar Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata, inda…

Shugaban Majalisar Wakilai Honorabul Yakubu Dogara, ya ziyarci kasuwanni da dama a garuruwa da kauyukan da ke Jihar Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya gana da ’yan kasuwa da masu gudanar da sana’o’in hannu kuma ya tallafa musu da kudi don bunkasa harkokinsu.

Shugaban wadda matarsa Gimbiya Dogara da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Misau/Dambam daga Jihar Bauchi Alhaji Ahmed Yerima suka rufa wa baya, ya ziyarci kauyukan Zwall da Burgel da Kagadaman Dass da Marabar Liman Katagum da  kuma Kadage da ke kan hanyar Bauchi zuwa Tafawa Balewa.

Malam Adamu Dan Ningi, wani mai sayar da nama a  Marabar Liman Katagum, ya bayyana cewa: “Shugaban ya ziyarci rumfata ya tambaye ni kudin tunkiya, na shaida masa Naira dubu 20 ne, sai kawai ya ba ni Naira dubu 20 ya ce in kara jari. Kuma zan yi amfani da kudin wajen sayo wata tunkiyar. Hakika shi mutum ne mai kyauta da yake taimakon jama’a ba tare da nuna bambanci ba, kuma mun sake tabbatar da hakan a yau.”

Wani mai suna Sabo Abdullahi kuwa cewa ya yi: “Shugaban ya ba ni kudi in kara jari. Shekaruna 37 amma ban taba ganin zababbe yana zuwa shago-shago da teburi-teburi yana tallafa wa jama’a da kudi ba su kara jari ba, ciki har da kananan ’yan kasuwa masu talla.”

Mutane da dama sun nuna godiyarsu kan yadda shugaban ya je har shaguna da teburansu yana ba su kudi su kara jari.

Honorabul Dogara yana sahun gaba wajen kiran a inganta harkokin qananan ’yan kasuwa da masu sana’ao’i domin a kawar da mugun talaucin da ake fama da shi tun daga yankunan karkara.

Ya yi gargadin cewa dimokuradiyya ba za ta bunkasa ba a yanayi na talauci da yunwa da tashi hankali da suke barazana ga dimokuradiyyar Najeriya.

A ranar Alhamis din makon jiya Shugaban Majalisar Wakilan ya tallafa wa maza da mata 526 bayan sun samu horo kan sana’o’i daban-daban musamman a harkokin noma.