✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogara ya sadaukar da kudin da aka tara don ranar haihuwarsa ga ’yan gudun hijira

Shugaban Majalisar Wakilai Honorabul  Yakubu Dogara, ya ce duk kudin da aka tara a wajen wasan kwallon kafa da abokansa suka shirya domin bikin cikarsa…

Shugaban Majalisar Wakilai Honorabul  Yakubu Dogara, ya ce duk kudin da aka tara a wajen wasan kwallon kafa da abokansa suka shirya domin bikin cikarsa shekarab 50 a ranar Lahadi za a mika su ne gaba daya ga ’yan gudun hijirar Najeriya.

Yakubu Dogara, wanda ya yi godiya ga abokai da abokan siyasarsa da suka halarci wasan ya ce yana fatan ya yi amfani da shekarun da Allah Ya ba shi a bayan kasa wajen kyautata wa jama’a su samu tsayawa da kafafunsu.

Ya ce:  “Duk abin da aka tara a lokacin bikin ranar haihuwar za a mika shi a matsayin sadaka. Kuma ya hada da kudin da aka tara wajen kaddamar da littafin, abin da muka yi a nan, shi ne duk abin da aka samu gaba daya za a mika shi a matsayin sadaka musamman don inganta rayuwar ’yan gudun hijirar Arewa maso Gabas, inda na fito.”

Ya kara da cewa: “A daidai lokacin da na cika shekara 50, abin da na fi bai wa muhimmanci ba shi ne tsawon kwana ba, ina son in ga yaya zan amfanar a wadannan shekara 50 da Allah Ya ba ni. Kun san idan kana raye za ka iya zabar kula da kanka ko kula da sauran jama’a.  Ina jin samun girma ya shafi yadda ka yi wa sauran jama’a hidima, wannan ya sa nake son sadaukar da duk abin da muka tara a wannan biki don inganta rayuwar wadancan mutane da suka fada tarkon rikicin da ba su ne suka jawo shi ba, ba su san yadda aka faro su ba, abin takaici galibinsu rikicin ya cutar da su. Babu abin da za mu iya yi da za a ce ya yi kankanta ko yawa, idan aka kashe su wajen farfado da mutanen da aka dankwafar suka taso don cimma abin da Ubangiji Ya kaddara musu.” 

Tun farko shugaban bikin kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin dangote, Alhaji Aliko dangote ya yaba wa Shugaban Majalisar Wakilan ne kan yadda ya zabi ya tara kudi a ranar cikarsa shekara 50 domin tallafa wa ’yan gudun hijirar, inda ya yi kiran a bayar da taimakon kudi don wannan manufa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya ce, ana samun ci gaba a aikin sake gina Arewa maso Gabas, inda ya yi fatar nan da dan kankanen lokaci za su koma gudanar da harkokin rayuwarsu kamar yadda suka saba.

Da take magana a madadin ’yan gudun hijirar, Misis Amina Gwoza ta mika godiya ga Dogara kan amincewa da dokar raya yankin Arewa maso Gabas da yadda yake nuna damuwa da matsalolin da suke damunsu, inda ta yi fatar za su fara ganin alfanun ayyukan ci gaba da raya yankin Arewa maso Gabas nan da kankanen lokaci.