✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Diyyar biliyan shida: Fani-Kayode bai ba mu wasika ba

Kamfanin ya ce shi ma a shafukan zumunta yake jin labari

Kamfanin Media Trust ya ce har yanzu bai samu wasikar Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode da ke yawo cewa yana neman ta biya shi diyyar Naira biliyan shida ba saboda wani ra’ayi da aka wallafa a kansa a jaridarta ta Daily Trust.

Sakataren Kamfanin, Kabir Bala, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce rashin mika wa kamfanin takardar “na nufin ba mu san abin da [Femi Fani-Kayode] yake yi ba; mu ma a kafafen sadarwa da zamani kawai mauka gani”.

Tsohon ministan wanda ake wa lakabi da FKK, a cikin wata wasika da lauyoyansa Adeola Adedipe ya rubuta na neman kamfanin ya janye wani ra’ayi da ta wallaf a ranar 30 ga watan Agusta, 2020, sannan ta ba shi hakuri a wasu manyan jaridu guda biyu.

FKK, a cikin wata wasika da lauyoyinsa suka rubuta na neman cikin sati biyu Daily Trust ya janye wani ra’ayi da ta wallaf a ranar 30 ga watan Agusta, 2020, sannan ta ba shi hakuri a wasu manyan jaridu guda biyu.

Ra’ayin na Iliyasu Gadu, ya caccaki Fani-Kayode kan cin mutunci da barazanar da ya yi wa wakilijn Daily Trust Eyo Charles a wurin taron ‘yan jarida a garin Kalaba, Jihar Kuros Riba, saboda ya bukaci sanin manufar ziyarar duba ayyukan gwamnonin Kudu maso Yamma da tsohon ministan ke yi da masu daukar nauyinsa.

Adeola Adedipe, ya ce idan kamfanin ya ki yin abubuwan da ke zayyane a cikin wasikar da ba wasikar da bai kai wa kamfanin ba, to za su dauki matakin shigar da kara a gaban kotu.

Tuni dai reshen Jihar Oyo na Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta kaurace wa wani taron ‘yan jida da ya kira a garin Ibadan a ranar Litinin.

Kafin nan akalla sau biyu Fani Kayode na neman yafitar dan jaridar Daily Trust, Mista Eyo Charles da NUJ da ‘yan jarida daukacin al’umma kan cin mutuncin da ya yi wa dan jaridar a Kalaba.

Fani-Kayode a wata wasikar nadama da ya aike wa NUJ ya ce abin da ya yi bai dace da wani shugaba ba, kuma yana fata Mista Charles zai yafe masa.

Tsohon ministan wanda ya ce yana ‘yan jarida ba za su kaurace masa ba saboda abin da ya yi wa Charles, ya ce ya ji kunyar abun da ya aikata wanda ya taba mutuncinsa ya kuma kunyata iyalai da makusantansa.

Kwana biyu bayan nan ne aka ga wasikar da tasa ta neman a ba shi hakuri tana yawo a shafukan zumunta.