✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Diskon Dodoridon dundumdurundum!

Tumurguji, tumurguji, Kwafdin-kwafdi gwangwarin gwam!Gwam! Gwam!!‘Kuma sai muma samuma kussa,’ inji Michael Jackson mawakin Amurkawa‘Bana sai na hau tarwada a kogi,’ inji Dondon Haurobiyawa Tun…

Tumurguji, tumurguji, Kwafdin-kwafdi gwangwarin gwam!
Gwam! Gwam!!
‘Kuma sai muma samuma kussa,’
inji Michael Jackson mawakin Amurkawa
‘Bana sai na hau tarwada a kogi,’
inji Dondon Haurobiyawa

Tun daga kamawar watan Yawon-wuni na shekara ta dubu karamin lauje da sili da zagaye jaridar Dalilin-taronsu ke ta baje mana labarin ‘diskon rabon duhun dundumdurundum,’ inda a rana ta karamin lauje da kwanciyar magirbi ta baje mana dimbin damin Hauron Hasken Haurobiyawa da aka lamunci Baraden Bindiga. dimbin lamunin dai an ce ya kai Hauro gashin balama tsayuwa bisa kafa guda da tsayuwa bisa kafa guda. Kuma diskon Haurubja, babban birnin Haurobiya shi ya kwashi kaso mafi tsoka, yayin da Yawon-wala-walar Fullo ke da dan tsugulin kaso na Hauro malala gashin tunkiya babban lauje da manuniyar sama.
Wannan ‘disko,’ ai da yana haskaka kasar Haurobiya yadda ya kamata da ni zan jajirce wajen ganin Baraden Bindigar Haurobiya da ke rundunonuin doron kasa da na tsuntsayen sama da na teku duk sun biya basussukan su, don gudun kada a karke da ‘Basussukan wuni-wuni, irin na ’Yan uwan da ba su da wani’ sai wuni-wunin bargar ingarmar cinikin samfarera da kurkuridon Honda kirar Amurkawa da Japanawa, watakila ma da Indiyawa.
Haurobiyawa ka da ku jefa azargagiyar zargi a kan Gwamnatin Haurobiya wajen cefanar da Kamfanin Dundumdurundum ga jiga-jigan kasa da gungun maso kaso-kason wawanci, sannan ta kafa Disko, wato ruguntsumin kida a cikin duhundundumdurumdum. Akwai wata dabarar rashin dabara da ba za ku fasko ba, har sai nan gaba. Kada kuma ku ce Malam Dodo ya buge da suka-da-burtsatsen maganganun shaci-fadi don nuna adawarsa ga ‘diskon haskaka Haurobiya.’Ba kuma na nufin cewa, an tafka ta’asa a kwanon tasa ba, illa dai kawai ina da masaniyar cewa, “DAKAN dAKA, SHIkAR dAKA, TANKAdEN BAKIN GADO aka yi wajen cefanar da kamfanonin haskaka Haurobiya. Ko kuma dai an tsuwurwurta CUKUdI-CUKUdI, wata sabuwar hanyar cin kudi, a daidai lokacin da Sinawa ke cin kwadi.
Kodayake  a karatun wasikar jakin dawa da na gida, in an yi waskiya za a iya cewa Gwamnatin Haurobiya ta samar da kamfanonin ruguntsumin Disko ne domin an gano tasirin kade-kade da raye-raye wajen murmurewar majinyata da ke kwance warwas a farfajiyar Bokan Turai. Hujja a kan haka ita ce Jaridar Kallom-jeji da ake wallafawa a Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ta ruwaito labarin ruguntsumin kidan diskon da aka shirya wa majinyata a Farfajiyar Bokan Turai ta Abu Dhabi da zummar ganin sun murmure.
’Yan makaranta kun ga ke nan tunda Jam’iyya mai maganin zogi da radaddin ciwon kururungu ke jan ragamar mulkin Haurobiya, ai sai kawai a kyale Kamfanonin Disko su yi kidan su, su taka rawar su. Mu dai a biranen Dabo da Dikko KIdAN-KOKO ake yi mana. Da na bijiro da tambaya ga masana kan dalilin wannan kida, alhali ba na jin ana cewa ya damu da gaya koko-koko.’ Sai aka sanar da ni cewa wani gwanin kidan duhun dundumdurundum ne ke buga gangarsa, wai shi Kidin-kukan-koko, wai idan an murguda baki, an kan ga gilashi, ana ta yaren Ingilishi sai a ce KIdKO!
Ni dai na san Kidan-kukan-koko ba ya maganin tabahuwa, musamman jin cewa da zarar an fara kidan-koko daukacin tahunnan da ke birnin Dabo inda ba a dabo, sai aikin su ya tsaya cik. Shi ke nan babu sauran markaden kayan dundume kurururu da nikan garin hatsi.
Kai ni tun ina dan dugwi-dugwi, wani abokina kolon Malam ya taba ba ni labarin yadda ’ya’yan uwar dakinsa suka so kawo masa tarnaki wajen daukar makaman yin artabu da tabahuwa. Wannan lamari dai ya auku ne, a lokacin da abokina ya hadu da bahallatsar ’yar Gusun da birnin Shehu, wato mai wutsil-wutsil a cikin dan Adam. Da jin lamarin ya ta’azzara babu sauki, sai kwai kolon Malam ya garzaya zuwa gidan uwar dakinsa, amma cikin rashin sa’a, sai ya iske ’ya’yanta sun shirya ruguntsaumin biki, sun sanya faifan garmaho. Da jin haka sai ya lallaba ya jefa kokon bararsa, amma ina, sai ya ji karar kidan Turawa:
Tumurguji, tumurguji,
Kwafdin-kwafdi gwangwarin gwam!
Gwam! Gwam!
Ni dai taba labarta muku abin da ya faru ga abokina kolon Malam, tun cikin shekara ta dubu karamin lauje da manuniyar sama, a cikin darasin mu na ’Yan gyare-gyare.’’ ’Yan makaranta sai a yi bitar ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege, don tantacewa ko kidan diskon da aka yi mana ya zama masalaha wajen haskaka Haurobiya?
Batu na ingarman kwangiri, idan har mahukunta dsuka jajirce kan cewa, DISKO zai iya haskaka Haurobiya, sannan ya samar mana da makamashin dora sanwa a matsugunnan al’umma da masana’antu, to ni zan je in nemi Alhaji Surajo mai Asharalle ya zo ya buga mana kidan Waregaja:
Warwarwar Waregaja,
Kun ji kidan DISKON nan irin na Turawa
Alhaji danlami na Rimi Mashasha
Ya yi kudi ya kyale shaidanu!
Ba don kada ku jefa mini azargagiyar zargi ba, ko ku yi mini tashen “Kai Malam ka yi rawa, ban yi ba, ai da na dan kara muku nawa shargallen da ya fi na mai asharalle:
Kamfanonin Diskon nan irin na Holewa
Sun murmure suna dada morewa
Sun samu wuri sun kyale konannu!
Haurobiyawa mu yi fafutikar ganin an daina yi mana kidan diskon Dodoridon duhun dundumdurundum, ko don samun makamashin dora sanwa da sarrafa na’urori a masana’antu da haskaka cibiyoyin koyon watsattsake da buda wagagen littattafai, uwa-uba mu tallafi farfajiyar Bokan Turai. Domin ta haka ne kawai za mu yi maganin zaman kashe fatari da watangaririya a cikin gari, ko gararambar gararin gari. Idan ba haka ba, to an maishe mu GAJA, ko kuma haurobiya Jaga-jaga, a cewar wani mawaki da ya fi kamfanin Duhun dundumdurum jagwalgwala sunan kasar nan.
Lallai da sake an bai wa mai kaza kai da kafa. Idan har  mahukuntan Haurobiya suna da tabbacin cewa kamfanonin disko za su iya yi mana kidan hasken lantarki, to wajibi ne a tursasa su, su rika walkato mana haske a kai, a kai. Kuma akwai bukatar gwamnati ta himmatu ka’in da na’in wajen samar da hasken makamashin rana da iska da sarrafa tarin juji, har ta kai ga mun fara kurmusun Jamus a kamus, musamman a wannan lokaci da kafafen sadarwa ke baza yadda Gwamnatin Jamus ke biyan al’umma la’ada da zarar sun yi amfani da makamashin da ta samar musu a kan kari, sabanin yadda muke biyan kamfanonin Disko lada da la’adar kadago, amma babu biyan bukata.