✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Direbobin motocin haya za su fara biyan harajin N292,000 duk shekara a Legas

Hakan na nufin kowacce mota yanzu za a rika biya mata N800 a kullum.

Gwamnatin Jihar Legas ta sanya hannu a kan wata sabuwar doka da za ta tattare harajin da take karba wuri guda daga masu motocin haya a tashoshin mota da garejin Jihar.

An dai cimma yarjejeniyar dokar ne tsakanin gwamnatin Jihar da na Kananan Hukumomi da kungiyoyin sufuri daban-daban da kuma wasu hukumomin gwamnatin Jihar.

A cewar Kwamishinan Kudi na Jihar, Dokta Rabi’u Olowo, harajin, wanda aka yanke shi a N800, ya kunshi dukkan kudaden da hukumomin Jihar suke karba daga direbobin a matsayin kudin shiga.

Ya ce sabuwar dokar za ta fara aiki ne nan take.

Hakan dai na nufin kowacce motar haya za ta rika biyan N800 a kullum, wato N24,000 a kowane wata, jimlar N292,000 ke nan a shekara.

A cewar Kwamishinan Kudi na Jihar ta Legas, kafin wannan sabuwar dokar, bincike ya nuna cewa direbobin kan biya tsakanin N3,000 zuwa N9,000 a matsayin haraji a kullum.

Ya kuma yi zargin cewa akasarin kudaden zirarewa suke yi, ba sa shiga lalitar gwamnati, inda ya ce yana da kyakkyawan fatan hakan zai kai ga rage kudaden sufuri a Jihar.

Sai dai harajin bai shafi kudin tikitin da Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW) take karba ba.

Shugaban NURTW na Jihar, Alhaji Musiliu Akinsanya, ya ce kungiyar, tare da takwararta ta RTEAN ne suka nemi gwamnatin ta dunkule harajin da take karba waje daya don su samu sauki.

Ya ce dokar ta shafi harajin da gwamnati take karba ne kawai, ban da na kungiyoyinsu.

Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Kan Harkokin Sufuri, Mista Toyin Fayinka, ya ce dokar wani yunkuri ne na kawo sauyi da kuma zamanantar da harkar sufuri a Jihar.