✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Direbobin manyan motoci sun rufe hanyar Zariya zuwa Kano

Suna zargin ma'aikatan haraji da dukan daya daga cikinsu

Direbobin manyan motocin dakon kaya sun rufe hanyar da ta tashi daga Zariya zuwa Kano sakamakon dukan da suke zargin masu karbar harajin sitika na gwamnatin jihar Kaduna sun lakada wa daya daga cikinsu.

Sun ce sai da kafadar direban mai suna Malam Bawa Isa, ta goce a sanadiyyar dukan.

Sun ce lamarin ya faru ne a dai dai kauyan Zabi da ke gundumar Dogarawa a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Toshe hanyar wanda direbobin suka fara tun daga karfe 7:00 na safiyar Alhamis, ya kai har zuwa karfe 2:00 na rana ba a sasanta da su ba.

Hakan dai ya jawo cunkoson manyan motoci na tsawon kilomitoci da dama daga inda aka yi rigimar.

Sai dadi duk kokarin jin tabakin hukumar tattara harajin bai samu ba kasancewar ma’aikatansu ba su da takamaiman wajan zama a yankin.

%d bloggers like this: