Direbobi a yankin Kudu sun bukaci a rika ba su tallafi saboda zaman gida da haramtacciyar kungiyar IPOB ke tilasta musu a duk ranar Litinin.
Direbobin sun bukaci gwamnati ta rika ba su tallafin ko kuma su ’yan IPOB din saboda mawuyacin halin da suke tsintar kansu a ciki a lokacin zaman gidan.
- Takardun Pandora: Peter Obi ya musanta sammacin EFCC
- An kama fasto kan yi wa karamar yarinya cikin shege
Direbobin sun yi wannan kiran ne a yayin da suke zantawa da manema labarai a Umuahia babban birnin Jihar Abia a kan irin illar da zaman gidan ke haifar wa ga kasuwancinsu.
“Muna bukatar a tallafa mana duba da yadda wannan dokar ke hana mutane zirga-ziraga a duk lokacin da aka sanya dokar,” a cewar wasu direbobi.
Suka kara da cewa yawan tilasta musu zaman gida “ba karamar illa take mana a kasuwancinmu ba saboda duk lokacin zaman gidan ba a samun fasinja, ga shi yawancinmu ba motocin kanmu ba ne, karba muka yi mu rika biya a hankali.”
Da dama dai daga cikin direbobin sun ce sun mayar da ranakun zaman gidan a matsayin ranakun hutun dole.