✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direban mota ya buge ɗan sanda har lahira a Gombe

Direban motar ya tsere daga wurin da lamarin ya faru ba tare da tsayawa ko ba da taimako ba.

Rundunar ’yan Sandan Jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin jami’anta, Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP) Clement Yunana, bayan wani mummunan haɗarin mota da ya auku a yankin Tumfure na ƙaramar Hukumar Akko.

Lamarin mai ban tausayi ya faru ne a ranar Laraba, 17 ga Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, a gaban gidan Man Matriɗ da ke Tumfure.

A cewar sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya sanya wa hannu, a binciken farko ya nuna cewa wata mota da ba a tantance ba, ta fito daga hanyar Bauchi zuwa cikin birnin Gombe, ta buge ASP Yunana yayin da yake ƙoƙarin ketare titi.

Direban motar ya tsere daga wurin da lamarin ya faru ba tare da tsayawa ko ba da taimako ba.

ASP Yunana, wanda ya kai shekaru 50 yana aiki ne a ofishin ’yan sanda na Railway da ke ƙarƙashin rukunin ’yan sanda na Garin Bajoga a Jihar Gombe.

A cewar sanarwar an garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya, Gombe domin ba shi  kulawar gaggawa, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa sakamakon raunin da ya samu.

Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Gombe, Bello Yahaya ne ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da fara farautar direban da ya gudu domin tabbatar da an kama shi.

Haka kuma, ya roƙi al’umma da su ba da duk wata muhimmin bayani da zai taimaka wajen kamo direban da ya aikata wannan ɗanyen aiki.

Rundunar ta bayyana alhini da jimaminta bisa wannan babban rashi, tare da miƙa ta’aziyyarta ga iyalai, abokai da abokan aiki na marigayin.