✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Direban da ya buge ’yan Hawan Sallah a Kano ya shiga hannu

Direban ya tsere bagan da ya afka wa wadanda ke kallon hawan sallah a Kano.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani direba mai shekara 52 kan kisan mutum daya a yayin Hawan Sallah bisa tukin ganganci.

Bidiyon yadda direban ya buge mutane yayin hawan Sallar ya karade kafafen sada zumunta, lamarin da ya sanga jami’an tsaro fara bincike bayan da direban ya tsere.

A garin tukin ganganci direban ya afka wa dandazon mutane da ke tsaye suna kallon hawan Sallah da ake gudanarwa akan titin zuwa gidan gwamnatin jihar, wanda daga bisani ya tsere.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da mutuwar mutum daya, yayin da wasu hudu suka samu karaya daban-daban.

Kiyawa ya ce: “Mun samu korafi daga ’yan uwan wadanda abun ya rutsa da su.

“Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba da umarnin kai su asibiti.

“Likita ya tabbatar da rasuwar Zaharaddin Sani Mohammed, mai shekara 30 daga unguwar Tarauni.

“Mutum hudu sun samu karaya: Nabila Garba ta samu karaya biyu; Saddiqa Abdulrazaq, ita ta samu karaya; Aliyu Maza daga Hotoro ya karye a kafa; sai kuma Nasir Imrana da ya samu buguwa a kai.”

Rundunar ’yan sandan ta ce an mika wanda ake zargin Sashen Binciken Manyan Laifuka don gudanar da bincike kafin a mika shi ga kotu don yanke masa hukunci.

Kakakin ’yan sandan ya jinjina wa al’ummar jihar kan yadda suke bai wa rundunar hadin kai wajen ba su bayanai da ke kawo nasara wajen dakile ayyuka bata-gari a Jihar.