Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani direban tankar mai mai shekara 45, Dahiru Aliyu a unguwar Hotoro.
Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, shi ne ya fitar da sanarwar faruwar lamarin a ranar Talata.
- Kafin ranar Asabar za a dawo da sadarwa a fadin Jihar Katsina —Masari
- Zazzabin Lassa na ci gaba da barazana a Najeriya —NCDC
“Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin.
“Mun samu kiran wayar neman agaji daga wani mai suna Shuaibu Muhammad da misalin karfe 10:59 na safe, kuma take muka tura jami’anmu zuwa wajen da abun ya faru,” a cewarsa.
Ya kara da cewa, Aliyu ya shiga cikin tankin tankin motar ce domin wanke man da ke ciki, amma aka yi rashin sa’a ya makale a ciki har ya mutu.
“Tankar man na dauke da lambar DLD 411 XF,” inji Abdullahi.