Wani direban mota ya kashe wani ɗan sanda mai muƙamin mataimakin sufeton ‘yan sanda (ASP) da ke aiki da rundunar ‘yan sandan Jihar Ekiti.
Bayanai sun ce direban wanda tsere ya murƙushe jami’in ɗan sandan mai suna Idris Lawal har lahira a wani shingen binciken ababen hawa da ke garejin Ayemi daura da titin Iworoko a Ado-Ekiti, babban birnin jihar.
- An ba da belin masu zanga-zangar tsadar rayuwa kan naira miliyan 10
- ASUU ta ayyana yajin aiki a Jami’ar Gombe
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da aikin bincike da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Litinin.
Duk da cewa an garzaya da jami’in zuwa Asibitin Koyarwa na Jihar Ekiti (EKSUTH) don duba lafiyarsa, likitocin da ke bakin aiki sun tabbatar da rasuwarsa.
Sanarwar da ’yan sanda suka fitar ta bayyana cewa direban yana cikin wata farar motar ƙirar Marsandi da ke tsala gudun wuce sa’a.
Rundunar ‘yan sandan ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike a ƙoƙarinta na cafke mai laifin.