Wani direban motar kabu-kabu da ba a bayyana sunansa ba, ya guntule wa kuma ya hadiye yatsan Iboko Kenneth, ma’aikacin Hukumar Raya Biranen Jihar Ebonyi.
Lamarin ya faru ne bayan wata takaddama da ta barke ranar Talata tsakanin direban da Iboko wanda ke aikin wucin gadi da hukumar raya birnin a banagaren kula da ababen hawa.
- Sanya takunkumi ya fi rigakafi zama kariya daga COVID-19 – Sabon bincike
- ’Yan bindiga sun koma amfani da wayoyin ‘oba-oba’
Kwamishinan Hukumar Raya Biranen Jihar, Cif Onyekachi Nwebonyi, ya bayyanawa ’yan jarida a Abakaliki cewa wannan aika-aikar da direban ya yi abin takaici ne, inda ya yi tir tare da Allah wadai da hakan.
A cewarsa, abin bakin ciki ne a ce direba ya yi fada da jami’in dake kokarin sanya birninJjihar a kan tsari, kuma har takai ga ya gutsure mishi yatsa ya kuma cinye.
Tuni dai aka garzaya da jami’in sashen bayar da agajin gaggawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Alex Ekwueme da ke Abakaliki domin samun kulawa.