✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Direba ya cinna wa kansa wuta saboda jami’an LASTMA sun kama motarsa

Wani direba ya banka wa kansa wuta saboda jami'an kula da zirga-zirgar ababen hawa na LASTMA a Jihar Legas sun kama motarsa.

Wani direba ya banka wa kansa wuta saboda jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa na LASTMA a Jihar Legas sun kama motarsa.

Jami’an LASTMA sun kama direban ne a kan laifin saba dokokin hanya, lamarin da ya sa ya yi ta ba su baki domin su yi hakuri.

Yana cikin ba su hakuri ne daya daga cikinsu ya shige gaban motar da karfin tsiya ya zauna a kujerar direba.

Ganau sun ce da direban ya ga haka, sai ya dauko wata jarka da ke cike da fetur a motar ya bulbula wa kansa fetur din, sannan ya cinna wa kansa wuta.

Shaidun  sun ce an ji direban yana cewa gara ya bar duniya da ya tsaya ya ga an tafi da iya abin da yake amfani da shi wajen rufa wa kansa asiri.

Ganin abin da ya faru, sai wasu direbobi da ke wurin suka shiga kokarin kashe wutar, wasu kuma suka yi ta jifan jami’an na LASTMA da duwatsu.

Ana cikin haka ne zauna-gari-banza da ake kira Arewa Boys suka zo wurin suka fara kai wa jami’an na LASTMA farmaki.

Hatsaniyar dai ta haifar cunkoson ababen hawa, a yayin mutane suka shiga guje-gujen neman tsira.

Wani direba da abin ya faru a kan idonsa ya ce an kai direban da ya cinna wa kansa wuta asibiti, “Amma ban sani ba ko ya rayu.”