Wani direba da karen motarsa sun yi wa wata matashiya mai shekaru 25 fyade a kasar Afirka ta Kudu.
Sun yi wa matashiyar mai dauke da cutar sida fyade kafin su jefar da ita a gefen hanya a yankin KwaZulu-Natal da ke Kudu maso Gabashin kasar.
- An harbe Shugaban Chadi, Idriss Deby
- Mazauna sun fusata bayan dakatar da Hakimi kan zargin rungumar baki a Abuja
Matashiyar mai suna Belram, ta bayyana wa jami’an tsaron Rusa cewa, ta ji tsoron sanar da wanda suka yi mata fyaden tana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.
Ta ce “tsoron rasa rai na ne ya hana ni bayyana musu cewar ina dauke da cutar.”
Beltram ta ce ta shiga motar ne don kai wa saurayinta ziyara, kamar yadda ta saba.
Kazalika, ta ce bayan daukar lokaci suna tafiya, ta tambayi karen motar dalilin rashin mutane a motar.
Wanda daga wannan lokaci ne ya sanya wani kyalle ya rufe mata baki, sannan suka keta mata haddi.
Sai dai, Kakakin ’yan sandan KwaDukuza, Nqobile Gwala, ya tabbatar da faruwar lamarin bayan an shigar musu da korafi a zargin a caji ofis na Verulam.