Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC), ta bukaci ma’aikatan lafiya da su zauna cikin shiri tare da binciko alamomin bakuwar cutar nan ta diphtheria.
Cikin sanarwar da ya bayar ranar Alhamis, Darakta-Janar na NCDC, Dokta Ifedayo Adetifa, ya ce hukumar ta samu rahoton bullar bakuwar cutar a Jihar Kano da Legas.
- NAJERIYA A YAU: Cutar Da Ke Ajalin Yara A Kano
- Za mu hukunta bankunan da ke boye sabbin kudade a Kano —CBN
Ya kara da cewa NCDC na ci gaba da lura da yanayi a jihohin Osun da Yobe inda nan ma aka samu bullar cutar.
Ma’aikatar Lafiya ta Kano ta ce kawo yanzu bakuwar cutar ta diphtheria ta kashe mutum 25 daga cikin 58 da ake zargin sun kamu da ita, yayin da mutum shida na nan ana ci gaba da kulawa da su.
A cewar NCDC, wasu kwayoyin cuta da ake kira da ‘Corynebacterium’ ke haifar da diphtheria wadda kan shafi hanci da makogwaro, wasu lokutan har da fata.
Alamominta
NCDC ta ce alamomin diphtheria sun hada da; zazzabi da yoyon hanci da bushewar makoshi da tari da rinewar idanu su zama ja da kuma kumburin wuya.
Wani lokaci idan lamarin ya tsananta, gefen makoshi kan yi kumburin da mai lalurar zai rika wahalar numfashi.
Adetifa ya ce NCDC na aiki tare da ma’aikatun lafiya na jihohi da sauransu wajen fadada aikin yaki da wannan cutar.
Masu fuskantar hatsarin kamuwa da cutar
Shugaban NCDC ya lissafo wadanda suka fi fuskantar hatsarin kamuwa da cutar da suka hada da:
• Yara da manyan da ba su yi rigakafin kariya daga kamuwa da diphtheria ba.
• Mutanen da ke zaune a wuri mai cunkoso.
• Mutanen da ke da zama a muhalli mara tsafta.
• Ma’aikatan kiwon lafiya da ke aikin kula da mutanen da suka kamu, ko ake zargin suna dauke da cutar.
Yaduwarta
NCDC ta ce bakuwar cutar ta diphtheria na yaduwa a tsakanin mutane cikin sauki, walau ta hanyar mu’amala da mai dauke da ita, feshi daga tari ko atishawar mai dauke da cutar da kuma ta’ammali da tufafi da abubuwa masu datti.
Hukumar ta shawarci iyaye da su tabbatar da an yi wa ’ya’yansu cikakken rigakafin cutar kamar yadda yake a tsarin yi wa yara rigakafi.
Ta kuma shawarci duk wanda ya ga alamar wannan cuta a tare da shi ya killace kansa sannan ya sanar da mahukunta mafi kusa ko NCDC, ko wata cibiya mai alaka da kiwon lafiya.