✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dino Melaye ya zama dan takarar Gwaman Kogi a PDP

Ya lashe zaben ne bayan wata zazzafar fafatawa

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya lashe zaben fid-da gwani tare da zama dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP na Jihar Kogi.

Hakan sai na nufin shi ne zai tsaya wa jam’iyyar takarar Gwamna a zaben na ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Sanata Dino Melaye ya sami nasarar lashe zaben ne bayan ya doke abokan takararsa a zaben da aka yi zazzafar fafatawa a cikinsa.

Tsohon dan Majalisar Dattijan dai zai fafata ne da Usman Ododo, dan takarar kujerar na jam’iyyar APC a zaben da ke tafe.

An gudanar da zaben ne a Lokoja, babban birnin Jihar cikin tsattsauran matakan tsaro.

A cewar Shugaban kwamitin shirya zaben, kuma tsohon shugaban riko na jam’iyyar na kasa, Sanata Ahmed Makarfi, Dino ya lashe zaben ne da kuri’a 313.

Kazalika, Ilona Idoko Kingsley ne ya zo na biyu da kuri’a 124, sai Usman Mohammed Kabiru da ya samu kuri’a 121, yayin da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Abayomi Sunday Awoniyi ya sami kuria’a 77.

Shi kuwa Injiniya Musa Wada ya sami kuri’a 56 ne, Ojaja Gideon Enama ya sami kuri’a 5, sai Olufemi Olarewaju da ya samu kuri’a 2 kacal.

Sanata Makarfi ya kuma ce kuri’u shida ne suka lalace a zaben, yayin da wani lauya, Abdullahi Haruna (SAN) ya janye daga zaben kafin a fara kada kuri’a.