Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya cire kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kogi Ali Janga.
An cire mista Janga ne tare da wasu manyan ‘yan sandan rundunar ‘yan sandan jihar bisa guduwar wadanda aka kama da makamai kuma ake zargin cewa Dino Melaye ne ya ba su.