Bayan an kama su da bindiga kirar AK 47 da tsabar kudi, aka kuma titsiye su, wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

Sun tababatar wa ’yan sanda cewa sun karbo kudin ne daga wani shugaban ’yan bindga mai suna Tukur Rabiu (NASHARME) da suka kai wa bindigogi kirar AK47 guda shida a Dajin Rijana da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a Jihar Kaduna.

Da yake gabatar da su a ranar Juma’a, kakakin Runudnar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce, ”Sun kuma amsa cewa su ke yi wa wani hatsabibin dan bindiga da ke buya a Dajin Rugu a Jihar Katsina da Dajin Dumburum a Jihar Katsina, Abu Rade, safarar makamai.”

Ya ce shugaban wadanda aka kama din ya ce, “Ana ba shi ladar N100,000 a duk lokacin da ya yi safarar makamai, kuma ya sha kai bindigogi kirar AK 47 zuwa maboyan ’yan bindiga a sassan Najeriya daban-daban.”