Kungiyar ’yan kasuwa masu sayar da magani (NAPPMED) sun shiga yajin aiki a Jihar Kano har sai abin da hali ya yi.
’Yan maganin sun dakatar da harkokinsu ne bayan Kukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta rufe musu shaguna a Malam Kato da kuma Kasuwar Sabon Gari.
Sun sanar da shigarsu yajin aikin ne bayan sun yi sallah tare yin addu’o’in samun nasara daga Allah a shari’ar da ke tsakaninsu da hukumar.
Shugaban NAFDAC a jihar, Kashim Ibrahim, ya ce sun rufe shagunan ne domin ganin ’yan maganin sun bi doka sun koma Kasuwar Dangwaro.
- Rikici a kan tabar wiwi ya yi ajalin mutum daya a Gombe
- An kafa dokar haramta ɓoye kayan abinci a Katsina
A cewarsa, za a ci gaba da samar da shagunan a Kasuwar Dangwaro domin magance matsalar rashin isassun shagunan da ’yan maganin suke fakewa da ita a matsayin dalilin rashin komawarsu.
Amma a martaninsa, shugaban kungiyar a jihar, Muhammad Musbahu Khalid, ya bayyana cewa sabon wurin da ake so su koma na Dangwaro ba na gwamnati ba ne, kawai na wasu ne, so kawai ake a tsawwalawa ’yan kasuwar magani.
A cewarsa sun rufe shagunansu ne domin gwamnati ta san amfanin ’yan magani a jihar Kano.
“Mun dauki wannan mataki ne don nuna wa gwamnati fushinmu da rashin amincewarmu game da hukuncin da kotun ta yi. Hakan zai sa gwamnati ta san amfaminmu,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa kungiyar tasu za ta daukaka kara don kalubalantar hukuncin kotun.
“Daga lokacin da aka yanke hukuncin mun karbi kwafin shari’ar inda kuma lauyoyinmu suka garzaya kotun daukaka kara don kalubalantar hukuncin; kuma insha Allah za mu yi nasara a kotun gaba.”
Ya kuma yi watsi da batun da ake yi cewa ’yan kabilar Ibo ne masu sana’ar magani a Kano, inda ya ce, “Wannan zance ne maras tushe kuma zalinci ne. Muna so al’ummar jihar manyanta da kakana su sani an yi haka ne saboda zalunci.”
Musbaha Yahaya, ya ba wa marasa lafiya hakuri da cewar, lamarin ya faru ne ba don suna so ba, sai don ya zame musu dole.
Idan za a iya tunawa a ranar Juma’ar da ta gabata ne Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin Mai sharia Simon Amobeda ta umarci manyan dilolin maganin da su koma Kasuwar Dangwaro don ci gaba da kasuwancinsu.
Hukuncin kotun shi ya kawo karshen takaddamar da aka dauki tsawon shekaru biyar ana yi tsakanin hukumar NAFDAC da kungiyar ’yan kasuwar.