✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An haramta lodin mutane a motocin daukar dabbobi

Dillalan dabbobi sun yi dokar daukar bayanan motocin dabbobi za ta yi tafiya zuwa yankin Kudu

Hadaddiyar Kungiyar Dillalan Abinci da Shanu ta Kasa ta haramta lodin fasinjoji a motar daukar shanu zuwa yankin Kudancin Najeriya.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Mohammed Tahir, ya bayyana a wurin wani taro a Kaduna, cewa kungiyar ta dauki matakin ne don kare rayukan fasinjojin da ake jigilar su zuwa kasuwannin yankunan Kudu.

Ya ce, “Dokar ta haramta lodin fasinjoji fiye da kima a motocin jigilar shanun zuwa Legas da Fatakwal da sauran sassan Kudancin kasar nan.

“An yi tireloli da manyan motoci ne don daukar kaya kawai, ba mutane ba, amma saboda rashin mutunta mutane, sai ka ga motocin na jigilar mutane 20 zuwa 30 a abin hawa guda da dabbobi.

“Duk mun san abin da ya faru kwanan nan idan kungiyar tsaro ta Ametokun ta tsare wasu ’yan Arewa a motar daukar kaya, cewa tana zargin ’yan ta’adda ne.

“Sam ba mu ji dadin lamarin ba, shi ya sanya ma muka hana hakan yanzu,” in ji shi.

Ya kuma ce kungiyar ta bullo da wata dokar ta daukar bayanan kowace mota da za ta yi tafiya da kayayyaki zuwa yankin Kudu, da ma sauran sassan kasar nan.

“Bayanan da za a fara dauka sun hada da nau’in kayan da mamallakinsu, hadi da inda ta nufa, domin taimakawa wajen magance safarar shanun sata daga Arewa zuwa yankin Kudu.