Tsohon Darakta-Janar na Hukumar Bunkasa Kanana da Matsakaitan Masana’antun Najeriya (SMEDAN) Dikko Umar Radda, ya lashe zaben gwamnan Jihar Katsina na jam’iyyar APC.
Da ya ke bayyana sakamakon zaben, shugaban kwamitin gudanar da zaben Barista Kaka Shehu Lawan, ya ce Radda ya samu kuri’u 506 daga cikin kuri’u 1,805 da wakilan jam’iyyar suka kada.
- Zulum ya samu tikitin sake tsayawa takara ba hamayya
- An kashe mutum 17,000 cikin wata 5 a Amurka – Bincike
An dai gudanar da zaben fidda-gwanin ne a ranar Alhamis, a filin wasa na Muhammad Dikko da ke birnin Katsina.
Sauran masu neman takarar da suka shiga zaben fidda-gwanin jam’iyyar APC sun hada da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Mustapha Muhammad Inuwa wanda ya samu kuri’a 442 da Abbas Umar Masanawa, wanda ya samu kuri’a 436.
Sauran sun daha d tsohon Kwamishinan kasafin kudi na jihar, Faruq Lawal Jobe, wanda ya samu kuri’a 71, Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua, ya samu kuri’a 32, AIG Abdulkarim Dauda Daura (mai ritaya) kuri’a 7, Umar Abdullahi Tata, kuri’a 8, mataimakin gwamnan Jihar, Mannir Yakubu, ya samu 65, sai Ahmad Musa Dangiwa tsohon Manajan Bankin Jinginar Gidaje, da ya samu kuri’a 220.
An samu kuri’a 18 a matsayin wadanda suka lalace a yayin zaben.
Jim kadan kafin a fara gudanar da zaben, gwamna Masari, ya jaddada cewar ba zai nuna wani dan takara don a zabe shi ba, amma yana rokon wakilan jam’iyyar da su zabi wanda ya cancanta.
A bangaren jam’iyyar adawa ta PDP kuwa, Sanata Yakubu Lado Danmarke ne ya lashe zaben fidda-gwanin dan takarar gwamna da jam’iyyar ta gudanar a ranar Alhamis.
Shugaban kwamitin zaben, Mista Chika Nwozuzu ne, ya bayyana Danmarke a matsayin wanda ya lashe zaben fidda-gwanin da misalin karfe 12:55 na safiyar ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa Danmarke, ya samu kuri’a 740, inda ya doke abokin hamayyarsa Salisu Yusuf Majigiri, wanda ya samu kuri’a 257.
Wasu masu neman takara biyu, Arc. Ahmed Aminu Yar’Adua da Shehu Inuwa Imam, sun samu kuri’a 53 da 44.
Wakilai 1,117 da aka zabo daga Kananan Hukumomin Jihar 34 ne suka halarci zaben da aka gudanar a hedkwatar jam’iyyar da ke Katsina.
An samu kuri’u 10 da suka lalace, yayin da aka ce wakilai hudu da aka amince da su ba su kada kuri’a ba bayan an tantance su.