Tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, ta bukaci wata Babbar Kotun Tarayya da ta janye umarnin da ta bai wa Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) na kwace mata kadarorinta.
Ta shigar da bukatar ce tana mai neman Kotun ta dakatar da EFCC daga sayar da kadarorin da ta kwace mata.
- Mutum 26 sun saye kadarorin Diezani da aka yi gwanjonsu
- EFCC ta yi gwanjon kadarorin su Diezani a kasuwa
“An yaudari kotunan ne wajen ba da umarnin kwace kadarorinta ta hanyar danniya ko kuma rashin bayyana gaskiyar abin ga duniya,” in ji ta.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito EFCC na shirin sayar da kadarorin Diezani da ta kwace ga mabukata daga ranar 9 ga Janairu kamar yadda yake kunshe cikin sanarwar da hukumar ta fitar.
Wannan ya biyo bayan nasarar da EFCC din ta samu ne a kotu a lokuta daban-daban kan ta yi gwanjon kadarorin da ta kwace a hannun tsohuwar Ministar.
Sai dai kuma, a karar da ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/21/2023 da kuma kwanan wata 6 ga Janairu ta hannun lauyanta, Mike Ozekhome, Diezani ta bukaci alkalin kotun Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya ba da umarnin dawo mata da kadarorinta.
Ta ba da hujjar cewa umarnin da aka bai wa EFFC an yi hakan ne ba tare da wani hurumi ba.
Ta ce ba a yi mata adalci ba a duk shari’o’in da suka kai ga ba da umarnin kwace mata kadarori.
Karar da Diezani ta shigar cike take da zargin ba a yi mata adalci ba, dalilin ke nan da ta daukaka kara kan hukuncin.
Sai dai wani jami’in EFCC da ya samu ganin takardar karar da tsohuwar ministar ta shigar, ya fada wa NAN cewa galibin zargin da Diezani ta yi ba gaskiya ba ne.
A nata bangaren, EFCC ta nemi kotu da ta yi watsi da karar tsohuwar ministar.