An nada Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, DCP Tunji Disu a matsayin sabon Shugaban Tawagar Tattara Bayanan Sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT).
Matakin na ranar Litinin na zuwa ne bayan amincewar Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba.
- ‘Matakin dakatar da Abba Kyari izina ce ga ’yan sanda’
- Mai taimaka wa IPOB da kudade daga kasar waje ya shiga hannu
Kazalika, matakin na zuwa ne biyo bayan dakatarwar da aka yi wa DCP Abba Kyari daga aikin dan sanda a ranar Lahadi sakamakon tuhumar da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Kasar Amurka FBI ke yi masa na karbar cin hanci.
Cikin sanarwar da Jami’in Hulda da Al’umma na rundunar Frank Mba ya fitar, ya ce nadin DCP Disu zai fara aiki nan take, inda Babban Sufeton ke shawartarsa da ya kasance kwararre a kan aikinsa.
A Lahadin da ta gabata ce Hukumar Kula da Aikin Dan sanda a Najeriya ta dakatar da Abba Kyari daga aikin dan sanda sakamakon zargin hannun a wata damfara da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka ta FBI ke yi masa.
Hukumar ta dauki matakin dakatar da Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan ne bayan shawarar da Babban Sufeton ’Yan sanda Usman Alkali Baba ya bayar.
Kyari dai ana zargin sa da karbar cin hanci daga hannun shahararren matashin dan Najeriyar nan da ke fuskantar tuhuma a Amurka kan ayyukan zamba na duniya, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Ana zargin Hushpuppi ne da zambatar manyan kafanoni da kungiyoyin kwallon kafa da kuma daidaikun mutane a kasashensu na fadin duniya.
Wasu bayanai da matashin ya fada wa masu bincike na cewa ya taba bai wa jami’in dan sanda Abba Kyari wasu kudade domin a daure wani abokin huldarsa, zargin da Kyari ya musanta.
Hukumar FBI ta bukaci hukumomin Najeriya da su binciki Abba Kyari bisa zargin karbar wasu kudade a matsayin cin hanci daga hannun Hushpuppi domin ya garkame masa wasu daga cikin abokanan huldarsa.