Matafiya da ke zirga-zirga a babbar hanyar Gusau zuwa Funtuwa sun shiga tasku sakamakon dawowar sace-sacen mutane da wasu ’yan bindiga ke yi a kan hanyar.
Babbar hanyar mai tsawon kilomita 100 kusan dai ita kadai ce hanya tilo da ke kai matafiya zuwa jihohin Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Katsina da sauran jihohin Arewa da dama.
- Gwamnati na kashe $10m wajen ciyar da dalibai miliyan 10 —Ngige
- Jerin ’yan kwallo 10 da suka samu kudi mai tsoka a 2022
Matafiya sun shaida wa wakilinmu cewa daga ranar Lahadin da ta gabata zuwa yanzu, ’yan bindigar da suka kafa shinge sun tare hanyar tare suna yin garkuwa da mutane.
An yi garkuwa da matafiya da dama yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga a cikin kwanaki biyar da suka gabata.
’Ya daban daji dauke da makamai suna tare hanya da rana tsaka, sabanin al’adar da suka saba yi a baya ta tare matafiya da safiya ko maraice.
A ranar Juma’ar da ta gabata ma dai an samu rahoton cewa da safe ne wasu masu ababen hawa da dama suka makale bayan da ‘yan ta’addan dauke da makamai suka tare wata hanya tsakanin kauyen Magazu zuwa ’Yankara a Jihar Katsina.
Tun da farko dai ’yan bindigar sun tare hanyar ce tare da kame matafiya a wani wuri mai nisan kilomita kadan daga kauyen ’Yankara da ke Karamar Hukumar Faskari ta Hihar Katsina.
“Mutanen Sakkwato, Kebbi da Zamfara masu son tafiya Katsina, Kano, Kaduna da sauran jihohin Arewa da dama, har ma da Kudu, ba za su samu wata hanya ba face su fasa tafiyarsu.
“Domin daya hanyar, wato wadda ta ratsa Gusau zuwa Kauran Namoda zuwa Zurmi zuwa Jibia, ta kasance a rufe na tsawon lokaci saboda ayyukan ’yan fashi da makami.
“A hakikanin gaskiya, hanyar ba ta da aminci ga matafiya a yanzu,” in ji wani mazaunin garin mai suna Aliyu Sani.
Shi ma wani matafiyi ya ce, “A ranar Alhamis, ina cikin tukin mota zuwa Kaduna a kan hanyar, kwatsam sai na hango masu ababen hawa suna jujjuyowa a yunkurin tsere wa ’yan bindigar.
“Sun bude wuta kan motocin da suka ki tsayawa.
“Muna kira ga hukumomi da su duba yiwuwar kafa shingayen binciken ababen hawa a kan titin, musamman ma wuraren da a al’adance suka kasance tarkon fada wa hannun masu garkuwa da mutane.”
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, sai dai bai amsa kiran wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.