Yayin da wasu daga cikin al’ummar Kano suke kuka cewa dawowar sanyi karo na biyu ya dagula musu lissafi, manoman alkama murna suke yi saboda amfanin da za su samu.
A tattaunawarsu da Aminiya, wasu manoma sun ce addu’arsu ce ta karbu, kasancewar kullum cikin rokon Allah suke a samu yanayi mai kyau da alkama za ta yi albarka, saboda halin kuncin da talakawa ke ciki.
- Ku ci gaba da karbar tsofaffin kudi – El-Rufa’i ga ma’aikatun gwamnatin Kaduna
- Yanzu matsalar canjin kudi ba za ta shafi zabe ba – Shugaban INEC
“Gaskiya ina farin ciki da dawowar sanyin nan, saboda irinmu da dama ba mu yi shukar alkamar da wuri ba.
“Sai dai fatan Allah Ya ci gaba da kawo mana sassauci a fita daga mawuyacin hali da ake ciki a Najeriya,” in ji Musa Yunusa, wani manomi a Kano.
Shi ma dai Inusa Haladu, cewa ya yi dawowar sanyin zai taimaka kwarai wajen sanya alkama ta wadata a kasa, kuma hakan zai taimaka wajen saukowar farashin kayayyakin da ake sarrafawa da ita.
“Kin ga kamarsu fulawa da abincin dabbobi da ita kanta tsabar alkamar, za su sauko a samu saukinta, manomi kuma zai yi ciniki ya samu abin rike iyali, haka shi ma dan kasuwa da zai sara ya sayar, kin ga tattalin arziki ya bunkasa ke nan.”
A hannu guda wasu sun bayyana cewa, sanyin ya dawo ne a lokacin da ake fama da yin sammako ko ma kwana a wuraren cire kudi, saboda karancinsu da ake fama da su.
Wata mata da Aminiya ta tarar da ita tana bin layin cirar kudi a unguwar Gyadi-gyadi ta ce da a ce sanyin zai sanya gwamnati ta tausaya ta saki wadataccen kudi, da ta yi farin ciki duk ba abu ne da aka saba gani ba a baya.
“Gaskiya dai a baya damina ce take yin haka, za ta dan lafa har sai an fara zafi sai kuma ta dawo. To bana kuma sanyi ne ya zo da haka.
“Kuma da ya tashi dawowa ma, sai ya dawo da hazon da ya fi wanda aka yi a farko.
“To gaskiya dai haka a cikinsa din muke baro ’ya‘yanmu mu zo nan wajen ana idar da Sallar Asuba, jikina na bari ga mura, amma haka za mu hau layin cirar kudi, to yaya za mu yi an jefa mu a wahala?
“Idan ba mu yi ba ya za mu yi da ’ya‘yanmu da zuwanmu aiki?
Shi kuma wani dattijo mai suna Malam Audu Tudun Wada cewa ya yi, da alama dai sauyin yanayin da ake ta fada ne ya juyo kan Najeriya.
“Ai bayan Kano kamar yadda na ji a labarai akwai wasu jihohin ma, kin ga dai mu a baya ba haka muka sani ba, to amma zamani ya sauya, shi ma yanayin zamani yake bi.
“Muna ta ji ana kukan yadda hayaki da kurar ababen hawa ke kawo wannan matsalar jin ta kawai muke yi amma ga shi mun gani.
“Don haka ko muna so, ko ba ma so, Allah Ya gama kaddara yadda Yake so, sai dai mu yi fatan ya ba mu wucewa lafiya kawai.”
Shi ma dai wani malamin makaranta, Hussaini Zubair, cewa ya yi dalilin rashin jin dadin dawowar sanyi a gurinsa, bai wuce dawowar makara tsakanin dalibai da ma’aikata ba.
“Dalibai a Jihar Kano na da dabi’ar makara sosai a lokacin sanyi da damina.
“A Kano ne za ki ga duk ranar da aka yi ruwa da safe zuwa kamar karfe 9:00, ko saboda sanyi kowa zai bai wa kansa hutu.
“Idan kika je jihohi irinsu Legas ba haka abin yake ba, ana ruwa kowa na hada-hadarsa, amma banda Kano da ke kiran kanta da tumbin giwa.
“Kin ga yanzu haka muke fama da makarar yara, sai iyayensu su ki kawo su da wuri, ka yi magana su ce sanyi zai sa mura ta kama ’ya’yansu.
“Kin ga wannan ba dalili ba ne, kasashen da ake musu dusar kankara kuma fa? Sai su daina karatu?
A hannu guda kuma, wani dan kasuwa da shi ma ya shirya yin tafiya ta jirgin sama zuwa Abuja, ya ce a da yana jin dadin dawowar sanyi, amma banda yanzu da tafiya ta kama shi, amma hazo ya hana.
“Gaskiya da na ji dadin sosai da dawowar sanyi, don na fi samun barci.
“Amma yau kam da hazo ya jawo min tafiya a mota zuwa Abuja da tsakar rana, na sauya shawara. Saboda kowa ya san dai hanyar zuwa Abuja sai a hankali.
“Banda haka ni ina jin dadin sanyi wallahi, na fi son sa da kowane yanayi,” in ji shi.
A watan janairu ne dai Hukumar Binciken Yanayi ta Kasa (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu jinkiri da karancin damina a jihohin Kano, Katsina, Jigawa, Yobe, Imo, Zamfara, Ribas, Kuros Riba a 2023.
Sai dai dawowar sanyin a wannan lokacin ya sha bambam da hasashen hukumar na cewa a Fabrairu iyakacin dararen watan ne kadai za a samu sanyi.