Al’ummar birnin Kano sun bayyana damuwa kan dawowar rikicin ’yan daba musamman bayan wanda ya wakana a yayin wani wasan a filin wasa na Sani Abacha da ke unguwar Kofar Mata.
Rikicin dai ya yi ajalin akalla mutum biyu, a yayin da ’yan daba dauke da muggan makamai suka rika kai farmaki a unguwannin Zango da Yakasai da ke kusa da Kasuwar Rimi, suna kwace da dukiyoyin jama’a.
Aminiya ta samu labarin cewa ma’aikatan Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ma ba su tsira ba, domin ’yan daban sun daba wa wata ma’aikaciyar jinya a asibitin wuka.
Malam Umar Tijjani mazaunin unguwar Yakasai ya bayyana damuwa kan yawaitar fargabar harin daukar fansa, lamarin da ya ce ya tilasta mutane zama a gidajensu bayan salla da almuru.
- Mai aikin shara ya mayar da N40m da ya tsinta a Kano
- DAGA LARABA: Me nasarar John Mahama ke nufi ga ƙasar Ghana?
Amma a kokarinsa na daukar mataki, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya ziyarci unguwannin tare da ba wa mazauan tabbacin cewa rundunar za ta murkushe ’yan daba da kuma samar da kwanciyar hankali.