Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP.
A cikin wata wasiƙar da Aminiya ta gani, David Mark ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar ne saboda rikice-rikicen shugabanci da aka gaza magancewa.
- Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana
- Kotu ta yanke hukuncin rataya ga dalibin da ya kashe malaminsa a Jos
Ya ce waɗannan matsalolin sun kawo wa jam’iyyar naƙaso kuma sun jawo mata abun kunya a idon jama’a.
A daren ranar Talata, an naɗa David Mark da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin shugabannin riƙon kwarya (Shugaba da Sakatare) na wata sabuwar jam’iyyar ADC.
Wannan jam’iyya wadda ta haɗa manyan ’yan adawa na da niyyar ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
A wasiƙarsa, Mark ya ce: “Na tsaya tsayin daka a PDP tun daɗewa, har lokacin da wasu suka bar jam’iyyar bayan faɗuwa zaɓen 2015.
“Amma yanzu jam’iyyar ta lalace, ba ta da tasiri ko haɗin kai. Bayan yanke shawara da iyalina da abokan siyasa, na yanke shawarar shiga sabuwar haɗakar siyasa domin ceto dimokuraɗiyya.”
Sabuwar haɗakar siyasar ta ce za ta ƙalubalanci Tinubu a zaɓe mai zuwa domin ƙwace mulki daga hannunsa.
Amma jam’iyyar APC mai mulki ta ce ba ta jin tsoron haɗakar da manyan ’yan adawa ke yi.
Muƙaddashin Shugaban jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, ya shaida wa BBC cewa babu wanda ke yin magana a kan wannan haɗaka sai a Abuja.
Ya ce: “Ba mu damu da wannan haɗaka ba. APC jam’iyya ce da mutane ke so. Sabuwar haɗaka ba ta da abin da za ta bai wa jama’a.”