A ranar Litanin, 9 ga watan Maris, 2015 da misalin karfe tara da minti ashirin na dare ne wani al’amari ya faru a cikin jihar Sakkwato wanda ba a saba ganin irinsa ba, wanda ni dai a tarihin rayuwata shi ne na farko da na shaida, wannan kuma ba komai ba ne face daurin auren abokina.
Idan aka yi la’akari da bangarorin biyu (mijin da matar) za ka ga cewar daurin aure ne gagarumi wanda baya ga dimbin ’yan uwa da abokan arziki da muka dade muna jiran wannan rana, manya-manyan masu fada a ji ne muke sa ran za su yi wa taron daurin auren dirar mikiya, in dai katse maka zance, hatta Gwamnan jiharmu ta Sakkwato, wajibi ne ya halarce shi, amma sai ga shi an daura shi a gaban mutanen da ba su fi ashirin ba.
Sirajo Shehu shi ne abokin nawa, wanda kuma dalibi ne da yake karatu a kasar Indiya, kuma ya dawo hutunsa ne na farko kawai. Sai dai kamar yadda Bahaushe yake cewa ”Aure mukaddari ne daga Allah” ashe Allah ya kaddaro Sirajo zai yi aure kafin komawarsa hutu duk da cewa shi bai tsara hakan ba, kuma babu wani mutum guda daya tak da ya tsara hakan.Wanda kuma kuma lalle wannan ba ya rasa nasaba da yadda muka dauki sha’anin larurorin aure da girma, muka dora su a muhallin da Allah da Manzon Allah ba su dora ba.
Yadda abin ya fara shi ne: Sirajo ya kira ni a waya da niyar mu hadu a kan yin shawara dangane da bukatar da yake da ita a ransa. Wannan bukatar kuwa ita ce, yin aure domin ya kare kansa daga ababen da ya ga suna kai kawo marasa kyau a tsakanin al’umma, musamman ma dalibai masu karatu a kasashen ketare. A karshe mun amince da cewar ya kamata ya nemi a aura masa yarinyar da suke son juna da ita, kuma suka amince a kan cewa za su auri juna idan Allah ya nufa, amma dai kawai za a daura auren ne a yi shagulgulan biki sai ya dauki matarsa zuwa Indiya inda zai ci gaba da karatunsa tare da ita a can hankali a kwance.
Cikin ikon Allah, bayan an dan kai-ruwa-rana, ‘yan uwansa suka amince da bukatarsa a kan cewa za su nema masa auren wannan yarinya kuma a bisa sharadin da muka ajiye. Sharadin shi ne, ba za a wahalar da ‘yan uwan amarya da yin wasu kayan daki na gaugawa ba tunda abin ya zo kwatsam (duk da cewar Allah ya hore musu abin da za su yi haka). shi kuma a gefen angon, ba sai ya tanadar wa amaryar gida kai tsaye ba, illa dai za a daura musu aure ne,bisa ga ka’idoji na shari’a.
Abin da muke zato shi ne, a wannan rana da na ambata a sama, za a je gidan su yarinya ne a yanka wa yaro sadaki domin a saka ranar daurin aure.Ranar da za mu zo mu yi ruwa mu yi tsaki mu nuna farin cikinmu. Amma abin mamaki a wannan ranar, da misalin lokacin da na ambata, kwatsam sai ga waya daga abokina yana mai sanar da ni cewa “Ka zo don Allah, ga shi nan
ana daura aurena”. Ko da na je, sai na tarar da zancensa gaskiya ne.Ashe lokacin da dattijawansa suka je inda dattijawan yarinya suke, bayan sun koro musu bayani, kawai sai su wakilan yarinya suka yi la’akari da cewa, tunda dai wannan auren an nufi a yi shi ne kawai don Allah ba domin kowa ba,to a daura aure kowa ma ya huta. A yi lamirin cikin sauki a kare shi cikin sauki. Haka ko aka yi, yanzu haka maganar da nake yi da kai, Sirajo Shi ne mijin Saudah. Sai dai yadda muka tsara daban, yadda kuma Allah ya yi daban. Muna fatan Allah ya sa shi ne mafi alkhairi.
Ni dai a tawa fahimta, aure shi ne abu mafi saukin kullawa idan an kai zuciya nesa. Idan dai za a iya daura auren Sirajo da Saudah a cikin mintuna goma ba tare da an kashe naira dari wadda ba cikin kudin sadaki ba, to auren kowa ma za a iya daurawa a cikin saukin da ya fi haka, matukar dai akwai dattijawa irin na gefen Saudatu da kuma gefen Sirajo.
Amma kai me ne ne ra’ayinka a kan wannan aure?
Nasir Abbas Babi (08033186727)