✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daurawa Ya Ba Batagari Wa’adin Mako 2 su tuba ko su bar Kano

"Ko ku tuba ko Hisbah ta murƙushe ku," in ji Sheikh Daurawa ga '’Yan Kwalta' bayan ya dawo kan mukaminsa a Hisbah

Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ba wa masu yawon ta-zubar, da aka fi sani da ’Yan Kwalta wa’adin mako biyu su tuba ko kuma hukumar ta murkushe su.

Sheikh Aminu Daurawa ya ba da wa’adin ne jim kadan bayan ya dawo kan mukaminsa, bayan sun sasanta da Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda kalamansa na sukar samamen Hisbah kan ’Yan Kwalta suka sa shugaban hukumar ya yi murabus.

Sakon da hukumar ta wallafa a shafinta mai taken jan kunne ya ce, ya ruwaito Sheikh Aminu Daurawa na ce wa bata-garin, “Sati biyu kacal ga ‘yan kwalta ko ku tuba ko Hisbah ta murƙushe ku.”

A ranar Litinin da dare ne dai aka sasanta Sheikh Daurawa da Gwamna Abba a wani zama da Majalisar Hadin Kan Malamai da Kungiyoyin Jihar Kano ta jagoranta a gidan gwamnatin jihar.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa Babban Limamin Masallacin Kasa da ke Abuja, Sheikh Ibrahim Maqari da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Falgore, suna daga cikin wadanda Gwamna Abba ya turo domin su yi masa bikon Sheikh Daurawa.

Murabus Sheikh Daurawa daga shugabancin Hisbah dai ya bar baya da kura, inda aka yi ta kiraye-kiraye da rokon sa ya koma ya dora a kan nasarorin da hukumar ta samu a karkashin jagorancinsa, musamman a bangaren yaki da badala.

A Juma’ar da Sheikh Daurawa ya sauka, wasu ’yan daudu sun kai wa jami’an Hisbah hari a ofishinsu a Kano, baya ga wata dabdala da suka gudanar tare da karuwa domin murnar saukar malamin.

Tun ranar Alhamis a lokacin taron da Gwamna Abba ya yi da malaman Jihar Kano kan shirye-shiryen azumin Ramadan da ke tafe ne gwamnan ya soki yadda jami’an Hisbah ke kai samame a matattaran bata-gari suna yi wa bata-garin diban karan mahaukaciya, ba maza, ba mata, ake ta ce-ce-ku-ce.

Wasu dai na ganin gwamnan ya yi daidai domin gyara ne ya yi wa hukumar ayyukanta, saboda jami’anta suna wuce gona da iri.

A gefe guda kuma wasu na ganin gwamnan ya yi katobara, kuma kalaman nasa tamkar kariya ce ga masu ayyukan masha’a a jihar, da kuma fifita su a kan malamin, wanda suke ganin an ci mutuncinsa, musamman ganin cewa malamin ba ya wurin kuma gwamnan na da ikon kiran sa ya yi masa gyara ba a bainar jama’a ba.

Hasali ma tun watanni uku da suka wuce da abin ya faru Sheikh Daurawa ya sanar cewa sun gyara kuskuren, har sun hukunta wadanda suka aikata ba daidai ba.

Washegari, Juma’a da sassafe Sheikh Daurawa ya sanar cewa ya sauka da mukamin, saboda kalaman gwamnan, sannan ya ti wa gwamnan da gwamnatinsa  fatan alheri da samun nasara, matakin da wasu ke ganin ya yi daidai.

Wasu dai na zargin subul-da-bakan gwamnan ya yi na da alaka da dambarwar shahararriyar ’yar tiktok Murja Kunya, wadda ta tayar da kura bayan an fitar da ita daga gidan yarin da kotu ta ba da umarnin ta bayan hukumar Hisbah ta gurfanar da ita kan zargin lalata tarbiyya, koya wa yara karuwanci da kuma razana jama’a.

Da dama daga cikin jama’a na zargin akwai hannun gwamnatin jihar Kano wajen fitar da Murja daga gidan yarin ta barauniyar hanya, zargin da gwamnatin ta musanta.