✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daukar ’yar wasan barkwanci abokiyar takara ba zai amfane ka ba —APC ga Jandor

Kakakin Jam’iyar APC na jihar Legas, Seye Oladejo, ya ce zabo ’yar wasan barkwanci a masana’antar Nollywood, Funke Akindele, a matsayin abokiyar takarar dan takarar…

Kakakin Jam’iyar APC na jihar Legas, Seye Oladejo, ya ce zabo ’yar wasan barkwanci a masana’antar Nollywood, Funke Akindele, a matsayin abokiyar takarar dan takarar Gwamnan na Jam’iyyar PDP  Abdulaziz Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, na nuna takararsa wasan yara ce kawai ba da gaske yake ba.

A ranar Talata ne dai Jandor ya ayyana Funke Akindele wacce aka fi sani da Jenifa a matsayin abokoiyar takararsa, bisa amannar cewa za ta daga darajar takarar tasa a idon al’umma.

Oladeji ya ci gaba da cewa, “Wannan na nuna Jandor bai ba wa takarar tasa muhimmanci a zaben 2023 mai gabatowa ba, domin yaba wa wacce ba za ta kara wa takararsa komai ba daga kuri’un masu zabe.

“Nugu da kari, ya nuna rashin ingantattun ’yan siyasa a jam’iyyar tasu, tunda har suka gabatar da abokiyar takarar da ta shiga jam’iyar tasu gab da zaben fidda gwani.

“Na yi farin ciki da na ji cewa ’yar takarar mataimakin gwamnansu ta ce ta dakatar da aikinta na fitowa a  wasan kwaikwayo, na san ba iya shi kadai ta dakatar ba, domin a baya-bayan nan sunanata na ta yawo a kafofin sada zumunta bisa dalilai marasa kyau.

“Ba na shakkar mazauna jiharmu ta Legas ba za su lamunci wannan wasan kwaikwayon, domin sun san jagoranci abu ne mai muhimmacin da ke bukatar kwararru ba wai ’yan nanaye ba.

“Da haka na ‘ke taya Gwamna Babajide Sanwo-Olu da Mataimakinsa, Obafemi Hamzat murnar sake darewa karagar mulkin jiharmu tun yanzu.”