Mahaifiyar jarumar shahararren fim din ‘Jenifa’s Diary’, Funke Akindele, wadda ta zama abokiyar dan takarar gwamnan Jihar Legas a Jam‘iyyar PDP, ta rasu kwanaki kadan kafin zaben.
Kanwar Funke, Olubunmi Akindele, ce tasa nar da rasuwar mahaifiyar tasu suna Dokta mai suna R.B Adebanjo-Akindele, ta shafinta na Instagram a ranar Talata.
- Mutum 2 sun mutu, 17 sun kamu da zazzabin Lassa a Binuwai
- Belgium ta nada Tedesco a matsayin sabon kocinta
Shugabar mata ta PDP reshen Jihar Legas Alhaja Idowu Akinsaya ta ce “Duk da haka za mu ci gaba da yakin neman zabenmu, don kuwa rasuwar ta zaburar da mu tabbatar da burin Funke ya cika,” in ji ta.
A cewarta, mahafiyar Funke Akindele ta rasu ne a lokacin da suka fi bukatarta, saboda gabatowar babban zaben da suke fatan ’yarta ta zamo mataimakiyar gwamna.
Ta ce sun kadu da samun labarin rasuwar margayiyar tare da mika ta‘aziyarta a madadin matan jam‘iyyar baki daya.
Akinsaya ta kuma ce Adebanjo ta rasu ne a lokacin da suka fi buƙatarta, saboda gabatowar babban zaben 2023, da suke fatan ‘yarta ta zamo mataimakiyar Gwamna.