Kungiyar hadin kai ta Kano wato Kano Unity Forum ta aike wa Shugaba Buhari takardar karar Gwamnan Abdullahi Ganduje da ke shirin ciwo bashin Naira biliyan 300 daga kasar China.
Shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Othman Tofa ya yi zargin kumbiya-kumbiyar a batun rancen domin aikin jirgin kasa, wanda ya ce babu wanda ya san sharudda da ka’idojin da rancen ya kunsa.
“In banda ‘yan tsiraru a gwamnatin babu wanda ya san sharudda da ka’idonin yarjejeniyar da adadin kudin wanda ake ta nuku-nuku da shi.
“Kashin farko na kwangilar a kan biliyan 300 ko biliyan 828 da wasu ke cewa, na da ban mamaki. Dole a sauya wannan tunani”, inji shi.
Tsohon dan takarar Shugaban Kasar a tsohuwar jam’iyyar NRC, a cikin wasikar ya ce duba da bayanan yawan bashin da ake bin Jihar Kano daga Ofishin kula da Basuka na kasa, ba zai yiwu ta kara ciwowa ba.
Kungiyar ta ce muddin gwamnatin jihar ta yi biris da bukatarta to za ta dauki matakin shari’a domin hana aikin jirgin kasar.
Ta kuma tura kwafin wasikar korafin nasa ga Majalisar Tarayya da Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, domin sun hana Ganduje ciwo bashin, to za su su dauki matakin shari’a, domin hana aikin jirgin kasar.