Wasu dattawan Arewa, karkashin inuwar Kungiyar Farfado da Martabar Arewa (NRO) ta yi taron masu ruwa da tsaki a Jihar Kano don tattauna matsalolin da suka dabaibaye Arewacin Najeriya.
Kungiyar dai ta ce taron wani bangare ne na irin kokarin da take yi na dawo da zaman lafiya, ci gaba da kuma kima da martabar yankin.
Da yake jawabi yayin taron a Kano ranar Asabar, Shugaban Kungiyar ta NRO, Alhaji Gidado Mukhtar ya ce sannu a hankali yankin na rasa manufofin da ya shahara a kansu, inda ya ce akwai bukatar yin duba na tsanaki a kai.
Shi ma da yake gabatar da tasa makalar mai taken, “Arewa a jiya, yau da kuma gobe”, tsohon Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida (NOUN), Farfesa Abdallah Uba Adamu, ya ce da sama da yaruka 320, akwai bukatar hadin kai a yankin kafin a samu ci gaba.
Shi kuwa wanda ya taba takarar Shugaban Kasa, Alhaji Bashir Tofa jaddada bukatar yankin ya rika magana da murya daya.
Ya alakanta kalubalen da yankin ke fama da su da lalaci, hassada, keta, zaman kashe wando da kuma rashin aiwatar da manufofin ci gaba da mahukunta suka tsara.
Ya ce, “Mun zabi Shugabanni don su yi mana aiki amma sun bige da bautar da mu. Akwai dubban abubuwan da ba mu san yadda za mu magance su ba.
“Ba mu da hadin kai, ba ma son juna. Ina makomarmu in babu Najeriya,” inji shi.
“Mun fuskanci abubuwa da dama da suka kamata su zama izina ga Shugabanninmu su canza amma a banza. Saudiyya ta taba tsintar kanta a irin wannan yanayin, amma sakamakon daukar matakin da ya kamata, yau suna daya daga cikin kasashen da suka ci gaba,” inji Alhaji Musa Magami, shi ma wani dattijo da ya yi jawabi a wajen taron.