Jigo a Jam’iyyar APC, kuma kodinetan kamfen din zaben Tinubu/Shettima na zaben 2023 a Jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya mayar da martani ga Minista a Ma’aikatar Tsaro, Bello Matawalle, inda ya ce Dattawan Arewa sun fi karfin zama cima-zaune.
- Kisan sojoji a Neja: ’Yan ta’adda sun debo ruwan dafa kansu
- An sace dagaci da matarsa da ’ya’yansu 5 a Kaduna
Aminiya ta ruwaito a wata sanarwa mai taken, ‘Gwamnatin Tinubu: Kungiyar Dattawan Arewa, cima-zaune, ba wakiltar Arewa suke yi,’ wadda Matawalle ya fitar, inda a ciki kwatanta Dattawan na Arewa da cima-zaune.
A martaninsa, wanda ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, Sanata Marafa ya bayyana cewa maimakon bata sunan Dattawan na Arewa, da Matawalle ya zayyana nasarorin da Shugaba Bola Tinubu ya samu ne a yankin na Arewa da ma kasar baki daya a wata goman farkon mulkinsa.
Ya ce bata sunan dattawan yankin, wanda nan ne Shugaba Tinubu ya samu kuri’a mafi yawa bai dace ba, kuma ba zai haifar wa Shugaban Kasar, wanda a kullum yake aiki ba dare ba rana wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta kamar matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da sauransu da mai ido ba.
A wannan lokacin da muke ciki, a cewar Marafa, Shugaba Tinubu ya fi bukatar goyon bayan ma’aikatansa da jajircewarsu wajen samun nasarar aiwatar da alkawuran da ya dauke domin ciyar da kasar gaba.
Sanata Marafa wanda ya wakilci mazabar Zamfara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019 ya yi kira ga Minista a Ma’aikatar Tsaron da ya janye maganarsa, sannan ya nemi afuwar Kungiyar Dattawan Arewa da ma ’yan Arewa baki daya.
“Kusan mako daya ke nan ina ta samun kiraye-kirayen waya daga wasu muhimman mutane daga yankinmu na Arewa da ma jam’iyyarmu ta APC, wadanda suka san alakata da Shugaban Kasa.
“Sun shiga damuwa ne saboda wasu kalamai da Minista a Ma’aikatar Tsaro ya yi, wadanda idan ba a gyara ba, za su bata alaka mai kyau da ke tsaka Shugaban Kasa Tinubu da yankinmu domin za a ga kamar ministan ya ari bakin Shugaban Kasar ne ko kuma Fadar Shugaban Kasa.
“A takaice dai ko kana so, ko ba ka so, wadannan mutanen sunansu Dattawan Arewa, don haka sai dai an cire musu wannan matsayin ba, aibata su, tamkar aibata mutanen yankin ne baki daya.
“Ba al’adarmu ba ce aibata manya. Babu wata al’umma da ta san me take yi da za ta aibata dattawanta, ballatantana ma Arewa.
“A matsayina na daya daga cikin sanatocin da suka yi aiki sosai da Asiwaju a lokacin yana jagoran jam’iyyar kamar yadda ake kiransa a lokacin, tun daga lokacin da aka kirkiri jam’iyyar, har zuwa lokacin da aka yi zaben fid-da-gwanin ya fitar da tsohon Shugaban Kasa Muhammau Buhari a matsayin dan takara a Legas, da kuma kasancewata jigo da aka dama shi a tata-burzar da suka faru a Majalisar Tarayya a 2015 da 2019, da kuma abubuwan da suke faru a zaben fid-da-gwani na 2023, ina tabbacin cewa Shugaba Tinubu yana girmama Arewa, da ’yan Arewa da kuma dattawanta, kuma yana ganinsu da kima.
“Duk da cewa ni ba mai magana da yawun Shugaban Kasa ba ne, amma a matsayina na dan Arewa, kuma dattijo, sannan kuma jigo a Jam’iyyar APC, wanda ya yi aiki tare da Shugaban Kasa Bola Tinubu da Mataimakinsa, ina so in bayyana cewa wannan ra’ayin da Matawalle ya bayyana nasa ne, ba ra’ayin Shugaban Kasa, don haka a yi watsi da shi.
“Lallai Arewa, da ’yan Arewa da dattawan yankin ba cima-zaune ba ne a duk abubuwan da suka shafi kasar nan. Na san wannan shi ne ra’ayin Shugaban Kasa.”