✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dattawa Sun Kashe Matashi Domin Tsafi A Zariya

Dattawa sun yi wa matashin kisan gilla kwana biyu bayan zuwansa Zariya domin ziyarar mahaifiyarsa.

Dubun wasu tsofaffi hudu ta cika kan zargin su da yi wa wani matashi kisan gilla da yukurin cire sassan jikinsa domin tsafi a Zariya, Jihar Kaduna.

Aminiya ta gano cewa matashin mai suna Emmanuel Pius mai shekara 29, daga garin Warri na Jihar Delta, ya gamu da ajalinsa ne bayan ya ziyarci mahaifiyarsa a Zariya.

Mahaifiyarsa, Sarah Pius, ta shaida wa Aminiya cewa bayan isowarsa da kwana biyu ne ya fita da niyyar zuwa banki ciro kudi, daga nan ba a kara jin duriyarsa ba.

Ta ce an yi ta kokarin kiran shi ta waya amma ba a samun shi, har rubutaccen sako an tura amma haka ba ta  cim-ma ruwa ba.

“Daga nan ne na tafi wurin ’yan sanda don kai rahoto a babban ofishinsu da ke PZ, Sabon Gari, Zariya.

“Ina wurin ne sai na sami waya daga Ofishin ’Yan sanda na Samaru inda suka bukaci in je wurinsu.

“Bayan na je sun sa na koma na zo da dan uwan mahaifin yaron, inda suka sanar da shi cewa wasu dattawa gudu hudu ake zargi da kashe Emmanuel.

“Sun sanar da shi cewa wadanda ake zargin suna hannunsu…har sun nuna mini su kuma dukkansu dattawa ne wadanda sun yi jika da yaron,” in ji ta.

Sarah Pius ta shaida wa wakilinmu cewa wadanda ake zargin sun yi yunkurin yanke wasu sassan jikin dan nata, amma Allah Bai ba su sa’a ba.

Sai dai duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin ’yan sanda game da lamarin bai yi nasara ba.

Ya kira Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ta waya, amma ya ce masa yana halarar wani taro, zai kira daga baya.

Sai dai har ya zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoton babu wani karin bayani, duk da cewa har sake tuna mishi aka yi, amma shiru.