✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daso da Mai sana’a sun nemi afuwar masarautar Kano

  Fitacciyar Jarumar finafinan Hausa na Kannywood Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso da fitaccen jaumin barkwancin nan Musa Mai sana’a sun nemi…

 

Fitacciyar Jarumar finafinan Hausa na Kannywood Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso da fitaccen jaumin barkwancin nan Musa Mai sana’a sun nemi afuwar Masarautar Kano bisa rike takwayen masu da jaruma Daso ta yi a cikin wani fim na Hausa mai suna Sabon dan Tijara.

Aminiya ta rawaio cewa tun daga lokacin da wasu hotuna da ke yawo a kafar sadarwa ta intanet wanda suka nuna  Jaruma Daso rike da tagwayen masu wanda Sarki kadai ke rike su a tsarin Masarautar Kanon jama’a ke ta allawadai tare da nuna rashin dadinsu game da abin da jarumar ta yi. Sai dai a jawabinta na neman afuwa, Daso ta bayyana cewa ta rike wadannan tagwayen masu ne ba don cin zarafi ga masarautar ba “wannan rike masu da na yi na yi shi ne don raha kawai, amma ba don na bata ran wani ba. Lokacin da muka yi hotunan sai muka watsa su a shafukanmu na sada zumunta don masoyanmu amma ba do wani abu ba. kuma ina so jama’a su fahimci cewa masu n da an rike ba wai na gasken ba ne, ina za mu ga masun Sarki? Ni kuma a iya sanina ban san cewa mace ba ta rike tagwayen masu ba. Don haka ina neman afuwar Masarautar Kano tare da duk wani da bai ji dadin abin ba.”

Saratu Gidado ta kara da cewa “mun dauki hotunan ne a lokacin daukar fim, jama’a za su gasgata haka a duk lokacin da fim din ya fito.”

Shi ma a nasa bangaren mashiryin fim din Musa Mai sana’a ya bi bayan Daso wajen neman afuwar jama’a inda ya bayyana cewa ba su da niyyar wulakanic ga masaurauta sai ma manufarsu ta kara wa masrautar kima a idanun al’umma.

“Mun san irin kima da daraja da masauratar Kano ke da ita, hasali ma ita masarauta ce mai nuna asali tare da  ci gaban rayuwar al’ummarmu, don haka ba za mu taba yin wani abu don cin zarafin ta ba,  sai dai ma mu yi abin da zai kara jawo mata martaba da daukaka. Mu kanmu daga masarautar muke, mun san darajarta. Duk da haka muna neman afuwar wannan masarauta tamu mai albarka da sauran jama’a wadanda ba su ji dadin abin da muka yi ba,” inji Mai Sana’a.