✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyyah (3)

Assalamu alaikum. Ya ku ma’abuta bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, kamar yadda muka faro wannan sabon maudu’i, a makon jiya, mun tsaya ne a darasi na…

Assalamu alaikum. Ya ku ma’abuta bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, kamar yadda muka faro wannan sabon maudu’i, a makon jiya, mun tsaya ne a darasi na shida, daga darussa goma da muke nazarta daga bakin mashahurin malami, Ibni kayyim Al-Jawziyya. A yau kuma za mu ci daga daga darasi na bakwai:
Lokacinmu: Malam ya gaya mana cewa, a duk cikin al’amuran dan Adam, babu wani abu da ya kai muhimmanci da kimar lokaci. A cikin lokaci ne duk wani al’mari ke gudana ko kuma yake faruwa, abu mai kyau, mai amfani ko akasinsa. Ke nan, da lokaci ne mutum zai gudanar da al’amarin da zai kawo masa ci gaba, ya kawo masa nasara a rayuwa, musamman idan ya yi amfani da damar da lokacin ya ba shi cikin fa’ida. Haka kuma, da lokacin ne mutum zai girbi asara da rashi, idan ya yi kuskuren banzatar da damar da lokacin ya ara masa.
Haka kuma, bayanai gamsassu bisa hujja sun tabbatar da cewa, kowane al’amari na duniya yana da kayyadadden lokacinsa. Haka shi ma mutum dan Adam, yana da lokacin rayuwa, wanda Allah (SWT) Ya kayyade masa ya rayu. Akwai lokacin yarinta, lokacin kuruciya, lokacin tsufa da lokacin mutuwa. Haka ita kanta duniyar, an karkasa ta zuwa yanayi-yanayi da lokaci-lokaci. Misali, akwai yanayin damina da yanayin rani. Akwai lokacin hudowar rana da lokacin faduwarta. Ke nan akwai dare da rana, kuma kowane yanayi ko lokaci yana da abubuwan da suka kamace shi na musamman.
dan Adam, dole ne ya kula da yanayi da lokaci kafin ya ci gajiyarsa. Abubuwan da zai aikata da rana, sun sha bamban da wadanda zai aikata da dare, kamar kuma yadda abubuwan da zai aikata lokacin damina, suka sha bamban da wadanda zai aikata da rani. Haka kuma, abubuwan da zai aikata lokacin da yake da kuruciya, sun sha bamban da wadanda zai aikata a lokacin da ya girma, ya manyanta.
Babbar fa’idar da ake son mutum ya kula da ita a rayuwa ita ce, mutum ya yi amfani da lokacinsa daidai yadda ya kamata, bisa kula da abin da yanayin yake bukata da kuma yadda yanayin ko lokacin ya gabatar da kansa. Misali, lokacin kuruciya, babu abin da mutum ya kamata ya lura da aikatawa sai neman ilimi da koyon al’amuran rayuwa, wadanda za su amfane shi a rayuwarsa ta gaba. Ke nan, idan ya bata lokacinsa bai yi wannan ba, ya yi asarar lokacinsa da yanayin ke nan. Kamar manomin da ya ki share gona, ya ki shuka a lokacin damina, ya yi asarar wannan lokacin ke nan, domin kuwa idan rani ya zo, ba zai girbi komai ba na amfani, kuma ba zai samu damar shuka ko noma wani amfani ba a lokacin ranin, domin kuwa ya bar dama ta kubuce masa tun da damina.
Don haka, a wannan darasi na bakwai, malam yana kira da cewa mu daraja lokaci, mu aikata ayyukan kirki, wadanda suka dace da lokacin da muka samu, domin kuwa tafiya yake, ba ya jiran kowa. Kada mu sake mu banzatar da lokacinmu wajen aikata abubuwan da ba za su kawo mana amfani ba ga rayuwarmu.
kwakwalwarmu: Ita ma kwakwalwa tana da tasiri a tare da dan Adam, domin kuwa tana taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa ko ruguza ci gaban dan Adam. Kamar zuciya, ita ma kwakwalwa tana dauke da al’amura masu muhimmanci, domin kuwa da ita ake tunani da nazari, domin kulla hikimomi da fasahohin da za su taimaki mutum ya kirkiri abubuwan da za su tallafa wa rayuwarsa. Misali, da kwakwalwa ce ake inganta ko bunkasa ilimi, kamar kuma yadda da ita ne ake kulla dubarun tunkarar al’amuran rayuwa.
Malam yana kira da mu yi amfani da kwakwalwarmu wajen kirkira abubuwan alheri, ba na sharri ba, abubuwan da za su inganta mana rayuwa, ba wadanda za su cutar da mu ba. A lokacin da mutum ya yi amfani da kwakwalwarsa wajen haddasa fitina ko wajen yaudara da zambatar al’umma, lallai bai yi amfani da ita ba wajen kirki. A yayin da mutum ya yi amfani da kwakawlwarsa wajen kirkiro wata kimiyya wacce za ta taimaka wa al’umma, ko kuma ya zayyana wata fasaha da za ta fahimtar da mutane don inganta rayuwarsu, lallai sai a ce san barka, ya amfani kansa da al’ummarsa ke nan. Don haka, mu rika yin amfani da kwakwalwarmu wajen shuka alheri ba sharri ba.
Ayyukanmu: Aiki, shi ma ya kasu kashi biyu. Aiki mai fa’ida mai amfanar da mutum da al’ummarsa, shi ne aiki na kwarai, a yayin da aikin banza ko akin assha, shi ake kira da aika-aika, domin kuwa ba zai amfanar da mai aikata shi ba da kuma al’ummarsa. Ke nan, Malam yana kiranmu da mu kula da duk wani abu da za mu aikata da gabobin jikinmu. Kada mu yi amfani da gabobin jikinmu wajen aikata barna, sai dai gyara. Aikin kirki, shi ne zai taimaki mutum a cikin al’ummarsa kuma zai taimake shi a tsakinsa da Allah mahalicci.
Tunani mai kyau: Darasi na goma da Malam Al-Jawziyya yake kiranmu mu fahimta shi ne zikiri. Malamin yana nuni da cewa mu tsarkake tunaninmu, mu rika ambaton Allah da yin tunanin halittarSa da izzarSa da girmanSa. Ta hanyar ambaton Allah ne za mu samu fa’idar rayuwa, sannan mu kara sakankancewa da imani da Shi. Wannan tunani ko ambatonsa bisa nazari, zai kara mana kusanci da Shi, zai kara mana tsoron Shi. Haka kuma, ta hanyar tunawa da shi, za mu aikata abubuwan da Yake so, alhali rashin yin haka zai sanya mu shagaltu, mu banzatar da tuaninmu wajen al’amuran da ba za su amfane mu ba.
Muna rokon Allah Ya ba mu dacewa da rayuwa mai inganci, Ya ba mu sa’ar tafiyar da al’amuranmu na rayuwa cikin fa’ida da cin riba. Allah Ya kara albarka ga aikin Malam Al-Jawziyya, Ya ba shi gwaggwabar lada da sakamako mai kyau a lahira. Amin.