Mutane daban-daban sun bayyana yadda suka ji yayin da suke jinya a killace bayan an tabbatar da sun kamu da cutar coronavirus.
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna na cikin wadanda suka fadi yadda suka sha fama.
Shi ma Mohammed Atiku Abubakar, dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, a wani jerin sakwanni da ya wallafa a shafinsa na Twitter yana sanar da warkewarsa, ya ce ya koyi wasu darussa.
Ga uku daga ciki:
Dan-Adam ajizi ne
Mohammed Atiku Abubakar ya ce lokacin da annobar ta barke a China bai taba tunanin zai zama daya daga cikin mutanen da cutar za ta kama ba.
Wannan ya koyar da shi cewa dan-Adam ba zai taba sanin abin da zai faru da shi a rayuwa ba.
“Wannan na cikin darussan da ba zan taba mantawa da su ba”, inji shi.
Haduwa wuri guda
Darasi na biyu da Mohammed AtikuAbubakar ya ce ya koya shi ne yadda wannan cuta ta hade kan ’yan Najeriya da ma al’ummar duniya, talakawansu da masu hannu da shuni, wajen yaki da annobar.
“[Don haka] ko ma wadanne matsaloli muke fuskanta, bai kamata mu yanke kauna da kasarmu ba”.
Ana bukatar gyara
Mohammed Atiku Abubakar ya kuma ce wani abu da ya bayyana a gare shi a lokacin da yake killace shi ne yadda wannan annoba ta bankado halin tabarbarewar da bangaren kiwon lafiya na Najeriya da ma sauran kasashe masu tasowa ke ciki.
“Sakamakon barkewar wannan cuta”, inji shi, “mun fahimci bukatar samar da isassun kudi ga bangaren kiwon lafiya”.
A cewarsa lokaci ya yi da ya kamata a inganta bangaren kiwon lafiya na Najeriya domin al’ummar kasar ta amfana.
Mohammed Atiku Abubakar dai ya kwashe kwanaki 40 yana jinyar cutar coronavirus.