Darajar Naira a kasuwar canji ta farfado zuwa 441.25 a kowace Dalar Amurka a hukumance
A wasu lokuta a ranar Litinin, sai da darajar Dala a kasuwar canji ta fadi zuwa N425 kafin daga karshe ta koma N441.25.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Burodi Ya Hargitsa Rayuwar ’Yan Najeriya
- Na dukufa wajen magance tsadar kayan abinci —Buhari
- Jami’ar Bayero ta ayyana ranar komawar dalibai
Darajar Naira a kasuwar canjin ta karu zuwa 441.25 daga Naira N439.63 da aka canji Dala a farkon ranar Litinin din.
A lokacin da kasuwar ta tashi a ranar Juma’a, 14 ga Oktoba, 2022, farashin Dala yana N441.38, amma zuwa safiyar Litinin ya kai N439.63.
Kafin tashin kasuwar a ranar Litinin, Dala ta kai N442.50 kafin daga bisani ta tsaya a N441.25.