✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dara ta ci gida: ISWAP ta kashe kwamandojin Boko Haram 2 a Borno

An kashe Abou Hamza da Abou Ibrahim, wasu kwamandojin Boko Haram

A ci gaba da kai hare-haren da suke yi wa juna, ’yan ta’addan ISWAP sun kashe kwamandojin Boko Haram biyu a yankin Gaizuwa da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Wata majiya ta ce an kashe Abou Hamza da Abou Ibrahim, wasu kwamandojin Boko Haram kuma masu karfin fada a ji cikin kungiyar, ne bayan da mayakan ISWAP suka kai hari sansanin mayakan da tsakar daren 17 ga Satumban 2022.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, a ranar Talata, a Maiduguri, wani kwararre a fannin yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce an kashe kwamandojin ne a wani samame da ’yan ta’addan ISWAP suka kai kan sansaninsu.

Ya kara da cewa an gano gawarwakinsu a gidajensu da sanyin safiyar ranar 18 ga Satumban 2022.

Baya ga kashe kwamandojin na su ne kuma sai ’yan ta’addan Boko Haram 70 a rukuni biyu daga Mafa, Karkut, Shiwai, lawe Kanuriye, Kirwa da Amtifur aka tattara su domin kai hare-haren ramuwar gayya ga ISWAP din.

“Amma ’yan ta’addan Boko Haram, sun sake fuskantar wata mummunar wuta, inda suka kashe wasu da ba a tantance adadinsu ba,” inji shi.

Ya ce hakan ne ya sa mayakan na Boko Haram suka fantsama zuwa bangarori daban-daban, inda aka rika kame wasu da makamansu.

Ya ce sakamakon hare-haren da aka kai wa kungiyar Boko Haram a cikin watanni biyun da suka gabata, mayakan na cikin rudani tare da rashin tabbas da za su iya fafatawa da sojojin Najeriya da rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) a yankin Tafkin Chadi.