A wani abu mai kama da almara, ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani shugaban masu garkuwa da mutane.
Hatsabibin mai garkuwa da mutanen da ake masa inkiya da ‘Confirm’ ya ce gungun wasu garkuwa da mutane da ya je ya sayar musu da makamai ne suka yi garkuwa da shi kuma ba su sake shi ba sai da ya biya kudin fansa.
‘Confirm’ daya ne daga cikin ’yan bindigar da suka addabi babbar hanyar Kaduna-Abuja da Abuja-Lokoja inda suke garkuwa da matafiya.
A lokacin da ya je sayar wa wasu masu garkuwa da mutane makamai ne shugaban daya gungun, wanda ake wa inkiya da Buba Bargu ya sa aka yi garkuwa da shi sai da aka biya kudin fansa N1.5m.
Ya bayyana hakan ne bayan ’yan sanda sun cafke shi tare da masu garkuwa da shi, suka kuma gabatar da su a Abuja.
“Ba zan iya kirga sau nawa na yi garkuwa da mutane ba, domin suna da yawa sosai,” inji shi.
Ya ce akwai ma lokacin da a lokaci guda gungunsa suka yi garkuwa da mutum 20.
“Abin da zan iya tunawa kawai shi ne an yi garkuwa da ni ne bayan na kai musu [Buba] harsasai 90,” inji.
Buba Bargu mai shekara 35, ya yi kaurin suna wurin kashe mutanen da ya yi garkuwa da su.
Yadda aka yi garkuwa da ‘Confirm’
‘Confirm’ ya ce ya zama shugaban masu garkuwa da mutane ne bayan jami’an tsaro sun kashe shugaban gungun da mataimakinsa.
A cewarsu, Buba na da alaka da kungiyar Boko Haram.
Ya ce da farko ya dauka wasa Buba yake yi cewa ya yi garkuwa da shi, amma da ya fahimci cewa da gaske yake yi, sai ya yi yunkurin yin amfani da tsafinsa wanda yake ganin bindiga ba za ta kama shi ba.
“Ban dauka harsashi zai kama ni ba saboda ina da asiri.
“Na bugi kirji na ce ai bindiga ba ta ci na, amma duk da haka Buba ya harbe ni don ya tabbatar min da gaske yake maganar karbar kudin fansa,” inji ‘Confirm,’ rike da hannun nasa da Buba ya yi masa rauni.
Ya ce da ya ga haka sai ya kira yaransa suka kawo N1,555,000.00 daga kasonsa na garkuwa da mutane da kuma sayar da makamai, aka biya Buba a matsayin kudin fansa.
Ba sani, ba sabo
Ya ce yana da cikakkiyar masaniya kan rashin tausayin Buba, “Na taba ganin Buba ya yi garkuwa da mutum 55 cikin babbar bas a lokaci guda.”
Ya ce shi ma ya dade yana garkuwa da mutane har ya tara Naira miliyan 15.
Buba ya tabbatar mana cewa shi da yaransa na cikin ’yan bindigar da suka addabi manyan tituna.
Ya ce shekararsa uku yana harkar, wanda a baya yake yi a karkashin wani mai suna Buji, amma yanzu shi ne maigidan kansa.
“Rashin adalci a wurin rabon kudaden fansa ne ya sa muka babe da Buji, na je na kafa nawa gungun,” inji shi.
An malamin masu garkuwa da mutane
An kama masu garkuwar ne tare da wani mutum wanda shi ne malaminsu mai yi musu aiki duk lokacin da za su fita.
Malamin da aka gabatar tare da wasu mutum 23 ya shaida wa wakilinmu cewa matsin rayuwa ce ta sa ya amince ya yi wa masu garkuwa da mutane aikin addu’a da kuma duba.
An gurfanar da su ne a kan laifukan garkuwa da mutane, fashi da sauran manyan laifuka a Hedkwatar Sashen ’Yan Sanda na SARS mai yaki d ayyukan fashi da aka rusa da ke Abuja.
Malamin ya ce an sha ba shi rabonsa na kudaden fansar mutanen da aka yi garkuwa da su.
“Akwai lokaci guda da na samu N400,000; An kuma sha ba ni N100,000, N50,000, N30,000 da N10,000 wannan ba zai kirgu ba,” inji shi.
Ya ce, “Na dade ina malanta amma da abubuwa suka dagule mini sai na koma Jihar Taraba, a nan ne wasu kungiyoyi suka same ni da cewa suna bukatar addu’a.
“Da farko ban san irin sana’ar da suke yi ba sai daga baya na san cewa garkuwa da mutane suke yi kuma na ci gaba da yi musu aiki.
“Kafin su fita aiki za su bukaci in yi musu addu’a, in kuma duba musu ko akwai sa’a,” kuma su biya, inji shi.
Ya ce idan kuma za su je kasuwa ko wani wuri sukan kira shi ya yi musu duba ya gani ko ba za a samu matsala ba.
Da na sanin bokan ’yan bindiga
Sai dai ya ce kama shin da aka yi ya sa shi tuba inda ya yi kira ga mutanen Najeriya da su zauna lafiya.
“Kama ni da jami’an tsaro suka yi ya zaman min darasi, na sauya rayuwa kuma ba zan sake yi wa bata-gari aiki ba.
“Zan taimaka wa jami’an tsaro da addu’a domin ganin an kama sauran masu aikata miyagun laifuka,” inji shi.
’Yan sanda
Da yake jawabi, kakakin ’yan sandan Najeriya, Frank Mba, ya koka kan karuwar ayyukan ta’addanci da rundunar ke yaka, kuma ya ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen karya lagon miyagun a bana.
Ya ce kawo yanzu, a 2021 Rundunar ta kama mutum 43 da ake zargi da aikata manyan laifuka ta kuma kwace bindigogi 13, harsashi 248 da motocin sata biyu daga wurinsu.
Sai dai Frank Mba bai yi karin bayani kan yadda aka kama masu garkuwa da mutanen ba.
Magance garkuwa da mutane
Shugaban Sashen Tsaro da Shugabanci a Hukumar UNDP mai kula da cigaban kasashe masu tasowa na Majalisar Dinkin Duniya, Chukwuma ya ce ’yan sanda kadai ba za su iya magance matsalar ba; tilas sai bangarorin kasa sun taimaka.
Ya shaida mana bukatar Ma’aikatar Shari’a ta taimaka wajen wajen yanke wa masu garkuwa da mutane hukunci.
“Masu garkuwa da mutanen nan a cikin al’ummomi suke zama kuma an san al’ummomin.
“Me zai hana a tuntubi shugabannin yankunan ta yadda za su rika bayar da bayanan take-taken mutanen da ba su yarda da su ba?
“Idan aka jawo su jika ba za su bari miyagun su rika aiki a yankunansu ba,” inji shi.