Barista, me za ka ce game da sace ’yan matan makarantar Dapchi da ake zargin ’yan Boko Haram da yi mako hudu da suka gabata?
Eh, a gaskiya sace wadannan ’yan mata na Dapchi ba abu ne mai dadin ji ba domin ko dabba aka sace ba abu ne mai dadi ba, balle dan Adam da Allah Ya masa daraja, balle kuma mace mai raunine, ga shi kuma masu karancin shekaru. Wannan rashin tausayin ya kai in da ya kai ba abu ne mai kyau ba kuma babu dadin ji, domi tun lokacin da aka sace ’yan matan Chibok nake nuna bakin ciki da alhinina. In ka duba ai ba ma wai ’yan matan Chibok kawai aka sace ba akwai mutane da dama da aka sace a garuruwa da yawa na Jihar Borno. Akwai wadanda aka sace a Damasak da Bama da Gwoza da Baga da Kukawa to amma sace wadannan ’yan mata ya yi suna a duniya don haka ba abu ne mai kyau ba, ina fata wadanda suke aikata wannan abu su yi wa Alla su bari, domin yana tayar da hankalin iyayen yaran da sauran na jama’a.
To me kake ganin makomarsu zai kasance a inda suke?
To wannan wani abu ne da ya zama gaibu, babu wanda ya san halin da suke shiga ciki sai Allah sai kuma su wadanda suka sace su. To amma ga duk mai hankali ya ji irin wannan abu zai yi mummunan harsashe a kansu, tunda ya faru a kan ’yan matan Chibok ba sai na fada maka ba, kuma koda a ce yau duk an sako su, babu ko shakka za a killace su a kula da lafiyarsu da makomar akidarsu kafin su fara cudanya da jama’a. Don haka tilas ne mu rika tunanin lafiyarsu da tarbiyyarsu, su ne manyan abubuwan da suka kamata mu rika tunani a kai har zuwa lokacin kubutarsu tun daga kan iyayennasu har zuwa jama’ar kasa.
Kana ganin akwai alaka kan sace su da ta ’yan matan Chibok?
Kada ka raba daya biyu mutanen da suka sace ’yan matan Chibok su ne suka sace na Dapchi, duk akidarsu daya ce koda bangarori ne daban-daban manufa daya suka dauke su, ko don su yi garkuwa da su su samu kudin fansa daga gwamnati, ko a yi musayar fursunonin yaki da su ko a’a da nufin biyan bukata irin ta dan Adam da makamantansu. Ko kuma sun sace su ne domin su saka gwamnati kunya ganin cewa tana ikirarin cin galaba a kansu, kuma za a iya cewa suna sace su ne don cika burinsu na hana karatun boko, duk wadannan su ne musabbabin sace ’yan matan Chibok da Dapchi.
Wace hanya za a bi don magance sake aukuwar hakan a gaba?
Hanyar ita ce ta sulhu, gwamnati ta zauna teburin shawara da wadannan mutane a yi yarjejeniya, duk abin da suke bukata a yi musu idan kuma ba zai yiwu ba su sassauto a yi masu abin da za a iya. Ni da kasar Switzerland da kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), mun yi kai-komo a tsakaninmu da gwamnati da wadannan mutane har aka kai ga sakin ’yan matan Chibok sama da 40 a kashi na farko, daga baya aka zo aka yi kashi na biyu wanda aka sakin sama da 80, to ka ga komai idan an yi shi da lalama za a cimma nasara. Sai kuma sai abu na biyu shi ne a killace makarantun a sanya jami’an tsaro ta yadda zai kasance akwai cikakken tsaro a makarantun iyaye da dalibai ba za su ji tsoron komai ba. Kuma jami’an tsaro su rika aiki da bayanan da jama’a suke ba su a kan lokaci domin magance sake aukuwar haka a gaba. Kuma gwamnati ta inganta rayuwar matasa domin kare su daga shiga cikin irin wadannan kungiyoyi masu tsatssauran ra’ayi, ta samar musu da aikin yi su shagala da aikinsu, su rika samun abin hannunsu da zai rufa musu asiri.
Me ya ba ka karfin gwiwar daukar nauyin ilimin marayu da marasa galihu a wannan lokaci na matsin tattalin arziki?
Na fara daukar nauyin ilimin marayun da suka rasa iyayensu ne tun kafin rikicin Boko Haram, bayan na kwashe shekara 20 ina aikin lauya. Sai na killace wani wuri na fara koyar da yara marayu 36, duk wata hidimar karatunsu da abincinsu na dauki nauyinsu. To daga 30 har suka kai 50 duk kafin rikicin Boko Haram, muna nan tafe sai ga rikicin Boko Haram ya zo, kuma ban fasa ba sai ma na kara ci gaba domin yaran da aka kashe iyayensu a rikicin farko a shekarar 2009 na samu karuwar marayu na ci gaba da daukar nauyinsu har suka kai 250. Da rikicin ya yi kamari suna sai suka yi ta karuwa, yanzu muna da sama da 800, har na kai ga bude makarantar na sanya mata suna Future Prowss Islamic Foundation School, Maiduguri, wadda a yanzu haka muna da dalibai sama da 300 yayin da dalibai dubu biyu ke jiran samun shiga makarantar.
To iyaye mata kana samun goyon bayansu kan daukar nauyin ilimin ’ya’yansu?
Eh, s uma mun dauko hikimar sanya su a ciki domin na lura cewa matukar ana bai wa yaransu ilimi kyauta to ba ko wani lokaci ne za su bai wa yaron dama ya tafi makaranta ba domin za ka iske a wani lokacin ba su da kudin motar da za su bai wa yaron ko ba su da abincin da za su ba shi kafin ya je makaranta. Sai muka yanke shawarar cewa kowace uwar yaro ita ma ta zo a koya mata sana’ar hannu, kamar saka da dinki da harhada kayayyakin shafe-shafe na mata da turaren wuta da dinkin hula kuma mun dauki iyaye mata 300, don ba su tallafi kuma muka bude musu asusu a banki. Ka ga mun ba su tallafi ke nan ta yadda za su samu saukin rayuwa da abin da za su ci su tura yaro makaranta tun da ba ta kwana ba ce. To a haka muke daukar nauyin yaran cikin sauki suna turo su da yarjejeniyar za a koyar musu da ilimin zamani da na addini da harsuna iri-iri da sana’o’i.
Wa yake tallafa maka wajen gudanar da wannan aiki saboda hannu daya ba ya daukar jinka?
Ina samun taimako daga kungiyoyin na duniya irin su ICRC da UNICEF da UNHCR da sauransu kuma gwamnatin jiha tana tallafa mana, ka san gwamnatin jiha da wadannan kungiyoyi sun shigo ne saboda rikicin Boko Haram, sai suka tarar da ni ina daukar wannan nauyi sai muka hadu muka tafi tare. Idan ba ka manta ba Majalisar dinkin Duniya ta taba ba ni lambar yabo kan irin ayyukan da nake gudanarwa a karshen bara har ma ta ba ni kyautar Dala dubu 150 wanda ya zo daidai da Naira miliyan 54, to wannan kudi ma na sanya shi don tafiyar da makarantata da tallafa wa iyayen yaran.
Yaran dukansu marayu ne ko akwai wadanda ba marayu ba?
Akwai ’ya’yana da ’ya’yan wadansu malamai, mun yi haka ne domin marayun su sake don za su ga cewa akwai wadansu da ba marayu ba muna karatu da su, wannan ita ce dabararmu kuma muna samun nasara.
Yanzu malamai nawa ne a makarantar?
Akwai malamai sama da 30, akwai malamai 8 suna daga jami’a da wasu wuraren suna yi mana taimako wato aikin sa-kai, kuma muna da dalibai sama da 800, mun yaye 300. Akwai masu jirar shiga makaranta su 2000 kuma duk daliban da muke yayewa suna samun ci gaba zuwa sakandare, wadansu ma sun kammala sakandare. Akwai wadanda suka yi Kwalejin Barewa da Kwalejin da Kwalejin Sarauniya Amina da suke Zariya da Kaduna da Kwalejin Gwamnati a nan Maiduguri da sauran manyan makarantu.
Wane kalubale ka taba fuskanta wajen gudanar da makarantar?
Ban cika haduwa da kalubale ba sai dai wadanda ba a rasa ba domin akwai surutai irin na mutane tun lokacin da na fara yau shekara 11 ke nan cewa yaya za a yi ya iya wannan abu ai ba zai iya ba, haka nake ji nake kuma toshe kunnena har Allah Ya kawo mu wannan lokaci. Abin da nake la’akari da shi shi ne me zan yi da al’ummata za ta amfana da ni, kuma me zan yi wanda Ubangijina zai ba ni lada ko bayan na mutu, kuma me al’ummata za ta rika tunawa da ni ko bayan na mutu. To irin wannan gudunmawa na fi bayar da karfi a kai, kada ka manta ilimi shi ne ginshikin rayuwar dan Adam a duniyarsa da Lahirarsa wannan shi ne abin da nake la’akari da shi.